Gwamnatin Kaduna ta karyata rahoton da ake yadawa cea za ta rufe layukan sadarwa a jihar.
Sanarwar da kakakin Gwamnan Jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata ta ce gwamnatin jihar ba ta da shirin rufe layukan sadarwa ba kuma ba ta taba tunanin daukar makamancin matakin ba.
- An yi garkuwa da tsohon Manajan gidan Talabijin na Katsina
- Abin Da Ya Sa Matasa Ba Sa Rajista Don Yin Zabe
Muyiwa ya ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta tuntubi wata hukuma ta tarayya don neman a dakatar da harkar sadarwa ba kuma ba ta ba da umarnin datse hanyoyin sadarwa ba.
“Tana kira ga mazauna jihar da su yi watsi da jita-jitar da ke yawo, saboda labarin karya ne da wasu mutane ke yadawa don goga wa gwamnatin Kaduna kashin kaji.
“Gwamnatin Jihar Kaduna tana fitar da komai a fili game da harkokin tsaro.
“Idan hara aka ga daukar matakin rufe hanyoyin sadarwa ya zama dole to za a sanar a hukumance ta hanyoyin da suka dace,” inji sanarwar.