Iyalan Sarkin Gobir na garin Gatawa da ke Jihar Sakkwato, sun sanar da cewa kawo yanzu ba su samu labarin kashe mahaifinsu da rahotanni ke cewa ’yan bindiga sun yi ba.
Babban dan Sarkin Gobir, Janjunan Gobir ne ya bayyana hakan yayin da Aminiya ta tuntube shi kan labarin kisan mahaifinsu da aka ce ’yan bindiga sun yi.
- Harin sojin sama ya kashe kwamandojin Boko Haram 5 a Borno
- ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano
Ya ce “har yanzu ba mu da wannan labari domin a tun jiya [Talata] muka yi magana da ’yan bindigar bayan cimma matsaya.
Ya kara da cewar “mun yi za su kira mu karfe biyu na rana, kawai sai muka rika jin labarin, yanzu lokacin da suka ba mu ya wuce ba su kira ba, amma ba mu ji daga wurinsu ba har yanzu muna dai jira.
Wata majiya a masarautar ta ce an cimma matsayar za a biya kudin fansa naira miliyan 60 da babura biyar kafin a sako Sarki da dansa da yake rike.
Majiyar ta ce “yau [Laraba] ne aka yi za a kai masu kuɗin idan sun faɗi wurin da za a kai kuɗin amma har yanzu ga shi la’asar ba su kira ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan daya daga cikin shugabannin Gobir ya sanar da cewa ’yan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa sun kashe shi.
A cikin wannan makon ne dai aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman Gwamnatin Sakkwato ta biya ’yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.
Makonni uku da suka gabata ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da sarkin a yankin Kwanar Maharba, lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sakkwato.