Hukumar Ma’aikatar ’Yan sanda ta ce ba ta ikon hukunta babban sufeto janar na ’yan sandan Najeriya.
A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Hukumar, Mista Ikechukwu Ani ya fitar ta nuna cewa hukumar ba za ta saba wa ka’idojin dokokin da suka kafa ta ba da suka ba ta ikon daukar jami’an ’yan sanda aiki da kara musu girma tare da hukunta jami’an da ke aiki da rundunar ’yan sandan Najeriya.
“Hukumar tana mai sanar da cewa ikon da take da shi bai shafi ofishin sufeto janar na ’yan sanda ba. Karfin ikon da hukumar take da shi yana kunshe a sakin layi na 30 kashi na farko sashe na uku na kundin dokokin shekarar 1999”. Inji sanarwar.
Ani ya ce dokar da ta baiwa hukumar ikon daukan aiki da hukunta jami’an ’yan sanda ba ta baiwa hukumar ikon hukunta sufeto janar ba.