✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ya yi kadan’

Aluko ya ce a halin da ake ciki a Najeriya, babu wani mai cikakken hankali da zai yi murna da N70,000 a matsayin mafi karancin…

Kungiyar kare hakkin dan Adam  ta CLO ta yi watsi da Naira 70,000 da Shugaba Bola tinubu da kungiyar kwadago suka amince a matsayin albashi mafi karanci a Najeriya.

Daraktan CLO, Kwamred Steve Aluko, ya ce babu hujjar da za a amince da N70,000, saboda babu amfanin kirki da zai yi wa ma’aikaci, don haka dole a ki amincewa da shi.

Aluko ya ce a halin da ake cikin a Najeriya, babu mai cikakken hankali da zai yi murna don an kara mafi karancin albashin zuwa N70,000.

Kwamred Aluko ya ce, “Idan aka yi la’kari da irin tsadar kayayyaki da matsin tatalin arziki da ake ciki da sauransu a kasar nan, babu abin yin murna da karin mafi karancin albashin zuwa N70,000.

Dan gwawarmayan kare hakkin dan Adam din ya ce, “Kwatanta albashin ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da na masu mukaman siyasa da na Sanatoci, da na majalisar wakilai.

“Sannan ka kwatanta mafi karancin albashi a sauran kasashen Afirka da na Najeriya, za ka ga babu dalili kuma babu tunani a sa N70,000 a Najeriya.

“Uwa uba, ka dubi dimbin albarkatun da Allah Ya hore wa Najeriya a matsayin kasa, don ma’aikatan kasar sun cancanci a samu kyakkyawan rayuwa,” in ji shi.