Gwamnatin Jihar Borno, ta tababtar da rasuwar mutum 32 a ’yan ta’adda suka kai kauyen Mudu mai tazarar kilomita 45 daga Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge ta jihar.
A ranar Talata ne dai a aka samu bullar rahoton kisan mutanen, wanda Kakakin Gwamna Babagana Zulum, Isa Gusau ya ce mutum shida sun samu rauni yayin da biyu suka tsere.
Isa Gusau ya shaida wa ’yan jarida ranar Laraba cewa, “Gwamna Zulum na cikin kaduwa sosai kan kashe al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba.
“Gwamna ya kadu ne tun daga lokacin da ya samu labari daga bakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Borno, Mohammed Sige, wanda kuma shi ke wakiltar Kala-Balge, in da lamarin ya faru”, in ji Gusau.
Ya ci gaba da cewa, “Daga bayanin Dan Majlisar, matasa 32 ’yan ta’addan suka kashe, amma ba manoma ba ne, masu sana’ar gwangwan ne, wadanda a jihar ake kira a jihar da Kayan Ajaokuta.
Masu sana’ar dai kan tattara karafa su sayar wa kamfononin da ke sarrafa su.
Isa Gusau ya ce: “Matasan su shiga kauyen Mudu ne a Karamar Hukumar Dikwa domin samo tama da karafa, in da ’yan bindigar suka far musu, tare da raunta shida, biyu suka tsira.
“Rundunar sojoji tare da shugaban karamar hukumar Kala-Balge sun gano gawarwaki 14 wadanda aka daure aka harba daga kusa.”
Don haka ne a cewar Gusau Gwamna Zulum ke taya iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su jaje.
Ya kuma ce gwamnatin jihar za ta dauki matakin da ya dace da zarar bincike ya kammala.