✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ma tsoron kowa sai Allah – Shugaban Sudan

Shugban Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya ce tsauraran takunkumin da Yammacin duniya ta kakaba musu ne suka durkusar da tattalin arzikin kasarsa. Shugaba Al-Bashir ya…

Shugban Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya ce tsauraran takunkumin da Yammacin duniya ta kakaba musu ne suka durkusar da tattalin arzikin kasarsa.

Shugaba Al-Bashir ya furta wadannan kalamai ne a tashar talabijin ta gwamnatin Sudan a wani jawabi da ya yi ga al’ummar kauyen Sheikh Mekki na yankin Al-Jazira, inda ya ce akwai mutane masu dimbin yawa wadanda a yanzu haka suke ci gaba da kai ruwa rana don durkusar da kasarsu ko ta halin kaka.

Omar Al-Bashir wanda ya sanar da cewa sun shirya taron ne don ya yi musu bayani a kan babbar manufar da suka sa a gaba ta ci gaban kasaru, “Allah wadai da maha’intan jami’an da ke ci gaba da kai-kawo don ganin sun durkusar da Sudan. Rugujewar tattalin arzikinmu ta samo asali ne daga tsauraran takunkumin da yammacin duniya ta kakaba mana. Dukan wadannan kulle-kullen sun samo asali ne daga bukatar kasashen Yamma ta ganin bayanmu, amma ba za mu taba durkusa wa gaban kowa ba sai Mahalccinmu Allah. Kuma ba za mu taba yarda a nuna wa kasarmu yatsa b,” inji shi.

A ranar Talatar da ta gabata 25 ga watan Disamba aka gudanar da wata gaggarumar zanga-zanga a gaf da fadar Shugaban Kasar Sudan da ke Khartum, inda jami’an tsaro suka kama da yawa daga cikin masu boren.

Shugaba Omar Al-Bashir ya nuna bacin ransa kan matsalolin tattalin aziki da a yanzu haka suka tursasa masu zanga-zangar suka fara mamaye kasar Sudan da yunkurin “Neman Sauyi.”

Tun ranar Alhamis din makon jiya ne daruruwan mutane daga sassan Atbara da Port Sudan da Khartum suke zanga-zangar nuna bacin ransu kan yadda farashin kayan masarufi suke hauhawa sakamakon tashin gwauron zabo da Dalar Amurka ta yi, wanda hakan ya haifar da mummunar durkushewar tattalin arzikin kasar.

Hukomomi a Sudan sun sanar da cewa tun a lokacin da aka fara wadannan zanga-zanga a ranar 19 ga Disamban zuwa yanzu , akalla mutum 8 suka rasa rayukansu.

Amurka ta yi alkawarin dage takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba wa Sudan a 1997 sakamakon zarginta da “daure wa ta’addanci gindi,” a cikin watan Janairun badi kamar yadda kafar labarai ta TRT ta ruwaito.