Kungiyar masu wuraren shakatawa a Babban Birnin Tarayya Abuja, sun aike wa Ministan birnin, Muhammad Bello, wasikar nuna rashin maincewarsu da yunkurin hana sayar da giya a wurarensu.
Wasikar, wacce aka aike gabanin fara aiwatar da shirin Gwamnatin Tarayya na dakatar da cinikin giya a wuraren, ta tunatarwa da Ministan kan cewa Najeriya fa kasa ce da ke bin tafarkin Dimukuradiyya.
- Gwamnati ta yi wa daliban da ke karatu a Ukraine tayin guraben karatu a jami’o’in Najeriya
- Mutum 12 sun rasu a gwabzawar ’yan sa-kai da ’yan bindiga a Jos
Kazalika sun ce kamata ya yi ministan yayi aiki da dokar kasa ya tsawata wa ma’aikatansa da su dakatar da batun rufe wuraren shakatawar ta karfi da yaji, da zarar karfe 6:00 na yamma ta yi a Abuja.
A wata wasika da lauyansu Ifeanyi Remy Agu ya rubuta kan kara mai lamba CV/408/2008, da Shugabar lambun shakatawar Suez, Misis Amanda Pam, da wasu karin mutane 60 ne ke karar Ministan Birnin Tarayyar, sun bayyana aiwatar da dokar rufe wuraren shakatawar ta karfe 6:00 na yamma da ya ke yi a matsayin wanda ya saba wa doka.
Haka zalika cikin wasikar sun ce, “A matsayinmu na lauyoyinsu, muna jan hankalinka kan wannan batun da yanzu ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kan cewa barazanar rufe wuraren sana’ar mutanen da karfe 6:00 na yamma a Birnin Tarayya da karfin tuwo da ma’aikatanka na musamman kan sanya ido da tabbatar da bin doka, Ikharo Attah, ke yi wani sashe ne na karar da ke gaban kotu.
“Ya kamata a fahimci cewa Najeriya kasar Dimokuradiyya ce, kuma doka na saman duk wani son zuciya da fashin ma’aikatan Gwamnati. Kotu ta kuma bayar da umarnin shigar da sharuddan sasantawa kan lamarin, bayan bangarorin sun amince da ka’idoji da tsare-tsare,” inji Lauyan.
Barista Agu ya kuma ce, “Wadanda muke karewa, sun kadu da barazanar ma’aikatanka na musamman ya yi kan waccan dokar.
“Yallabai, a matsayin ka na Minista a bisa doron doka, muna rokonka da ka yi amfani da ofishinka don jan kunnen ma’akatan, musamman ganin yadda batun ke gaban kotu, kuma bangarorin sun amince da ka’idojin.”
Ya kara da cewa kasancewar an samu aikata laifuka a daya daga cikin lambunan, ba ya nufin sauran ma haka suke, da har zai janyo musu dokar rufe su da karfe 6:00 na yamma ba.