Masana harkar tsaro da masu ruwa da tsaki a Jihar Binuwai sun yi tir da kashe Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana, wanda sojoji suka bindige.
Wanin masanin harakar tsaro, Group Kyaftin Sadiq Shehu mai murabus, ya ce dokar kasa da ta kare hakkin jama’a na duniya na gaba da komai saboda haka babu hujjar kashe wanda ake zargi.
- Yadda aka kashe dan ta’addan da ya addabi Binuwai
- Buhai ya kaddamar da shirin kyutata rayuwa na musamman
“Idan ka tsare mutum to a koma karkashin ikonka kuma a matsayin kwararren soja ba ka harbin shi.
“Ba hurumin sojoji ba ne yanke hukuncin cewa Gana ba shi da amfani ga al’umma, aikin kotu ne”, inji shi a hirarsa da Aminiya ta waya.
A ranar Talata aka samu rahoto cewa sojoji sun kame Gana sun harbe shi, bayan sun tsare ayarin motocin da ke hanyarsu ta kai shi Makurdi, babban birnin jihar.
Amma sanarwar da hukumomin soji suka fitar ta ce sun bindige shi ne a musayar wuta taksanin su da shi da yaransa.
A bangare guda kuma Gwamna Samuel Ortom ya ce Gana wanda dan tayar da kayar baya ne na hanyar zuwa Makurdi ne tare da yaransa fiye da 100 domin a yi musu afuwa.
– ‘Akwai daure kai’ –
Group Kyaftin Shehu ya ce idan har abin da Ortom ya fada cewa an kama Gana ne da ransa, to kashe shin da aka yi abin Allah wadai ne.
Amma idan a musayar wuta aka kashe shi, kamar yadda sojoji ke cewa, to sojojin suna da ’yancin su kare kansu.
Shi ma Kabir Adamu, wani masani a harkar tsaro ya yi tir da zargin kashe shugaban mayakan sa kan ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa wajibi ne a bi doka a koyaushe.
Sai dai ya ce abin mamaki ne Gwamna Ortom na ganawa da mutumin da ake nema ruwa a jallo saboda kashe wani hadimin gwamna.
Gana tsohon shugaban ’yan sintiri ne da ake zargi yana amfani da mamakan da a baya gwamnati ta samar musu.
– ‘Kololuwar karya doka’ –
Kabir Adamu ya ce, wannan shi ne kololuwar karya doka, domin tun da har Ortom ya san ’yan sanda na neman Gana, to kamata ya yi ya sanar da hukumomin da suka dace game da inda mai laifin yake.
“Ana namen Gana ruwa a jallo saboda haka babu yadda za a yi masa afuwa ba tare da umarnin kotu ba”, inji shi.
Amma ya ce duk da haka babu dalilin a kashe shi ba bisa ka’ida ba kuma bai kamata a lamunci hakan ba.
Ya yi nuni ga jawabin ’Yar Aiken ta Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan Kisa Ba Bisa Ka’ida Ba, Agnes Callamard, da ke cewa sassan dokokin Najeriya na ba wa jami’an tsaro damar kashe mutane ba bisa ka’ida ba.
Don haka ya bukaci a yi wa dokokin gyara domin kawo karshen kisa ba bisa ka’ida ba.
Masanin ya ce akwai muhimman bayanai da Gana ke da su wadanda da ya bayar da su da za su taimaka wa hukumomin tsaron kasar.
– Martanin shugabannin Binuwai –
Wani shugaban al’umma a Karamar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai, Cif Joseph Awana ya ce kashe Gana da sojojin suka yi bai dace ba kuma manya Sankera da ke Kananan Hukumomin Ukum, Logo da Katsina-Ala sun yi takaici.
“Kashe Gana bai dace ba kuma mu dattawan Sankera ba mu ji dadi ba. Wannan kisa ba bisa ka’ida ba ne.
“Sun kashe shi ta mummunar hanya. Zai haifar mana da karin matsala”, inji shi ta wayar tarho.
Ya ce abin da aka yi wa Gana ya bambanta da yadda aka yi wa wasu tubabbun masu a sassan kasar, yana mai fargabar wasu yaransa da suka tsere bayan an kama shi na iya zama matsala daga baya.
“Ba mu san tabbacin da sojoji za su ba mu cewa yaran ba za su zo suna neman mu ba”, inji shi.
– ‘Damar bude sabon babi’ –
Wani shugaban matasa ’yan kabilar Idoma, Adakole, ya yi takaicin cewa abin da ya faru na iya sanyaya gwiwar masu laifi da ke neman su tuba.
A cewarasa, kashe Gana wanda tsohon shugaban mayakan sa kai ne da ya mika wuya domin rungumar zaman lafiya da shirin afuwar gwamnati na nufin masu laifi ba su damar sauya rayuwarsu ke nan.
Ya ce babu wata kariya da za a iya bayarwa kan ta’addancin Gana, amma da mamakin yadda shi aka kashe shi, alhali a wasu wuraren an yi wa tsoffin ’yan bindiga da suka addabi sassan kasar afuwa.
“Ina yin tir da kisan da aka yi wa Gana saboda ba za ka zo kawai ka kashe mutumin da ya mika wuya da kansa yake kuma shirin aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro da kuma sauya rayuwarsa ba”, inji Adakole.