Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati (EFCC) ta ce jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ba su kama mukaddashin shugabanta Ibrahim Magu ba, sun ba shi takardar gayyata ne kuma ya je.
Hukumar ta EFCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan rahotanni sun watsu cewa jami’an DSS sun kama shi, rade-radin da mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, ya musanta.
Sanarwar mai dauke da sa-hannun mai magana da yawun Magu, Dele Oyewale, ta kuma ce an aika wa Ibrahim Magun takardar gayyatar ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa hedkwatar Rundunar ’Yan Sanda ta kasa a Abuja.
“Ba a kama ko tilasta wa shugaban EFCC ya amsa gayyatar ba, kuma a tare da shi akwai wani jami’i daga sashen shari’a na hukumar”, inji sanarwar.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan zargin da ake yi cewa Ibrahim Magu ya sayi wasu kadarori guda hudu ya kuma yi amfani da wani mutum ya fitar da kudade waje.
An hana manema labarai shiga
Wakilinmu ya ruwaito cewa Magu ya amsa tambayoyi a babban dakin taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Manema labarai na Fadar Shugaban Kasar sun ce an hana su shiga dakin taron suna karin bayani da cewa jami’in hukumar DSS din da ya tare su da sanyayan kalamai ya ce musu ba za su shiga ba.
“Ku hakura da amfani da wannan wurin na yau,” inji shi.
An dai ba da rahoton cewa wani kwamitin da shugaban kasa ya kafa don ya binciki ayyukan hukumar ta EFCC ne ya gayyaci Magu don ya amsa tambayoyi.
An kuma ce an tsare Magu ne a cikin wani cunkoson motoci a gundumar Wuse II inda aka mika masa takardar gayyata kuma aka ki amincewa a ba shi lokaci kafin ya hallara.
Jami’an tsaron sun ce masa gayyatar kwamitin ta fi zuwa ofis dinsa muhimmanci saboda haka ya bi su zuwa Fadar ta Shugaban Kasa inda suka isa da misalin karfe 1:35.