Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce ba gudu ba ja da baya dangane da sabuwar dokar bankin na takaita amfani da tsabar kudi a hannun ’yan kasa.
Emefiele ya fadi hakan ne a matsayin martani ga ce-ce-ku-cen da ake yi game da sabbin dokokin cire kudin da CBN ya fitar wadanda za su fara aiki nan ba da dadewa ba.
Yayin zamanta a ranar Alhamis, Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnan CBN ya dakatar da aiwatar da wadannan sabbin dokokin har a ga yanayin karbuwar makamantasu da ke kunshe cikin Dokokin CBN da Kundin Tsarin Mulki na 1999.
Majalisar ta bukaci Emefiele ya bayyana a gabanta ranar Alhamis mai zuwa domin amsa mata tambayoyi dangane da tasiri da kuma alfanun dokokin.
Ita ma Majalisar Dattawa ta nuna damuwarta kan sabuwar dokar cire kudin da CBN ya fitar, inda ta ce za ta tattauna kan batun a ranar Talatar makon gobe.
Da yake yi wa manema labarai bayani jim kadan bayan ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis, Emefiele ya ce an samar da hanyoyin hada-hadar kudade na zamani da dama tun bayan kaddamar da dokar takaita mu’amala da tsabar kudi shekaru 10 da suka gabata.
Ya ce a baya an sha dakatar da aiwatar da tsarin domin samun zarafin yin cikakken shiri kan batun da kuma inganta tsarin yadda ake hada-hada da kudi a Najeriya.