✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba don mu karya mutane muka kirkiro canjin kudi ba – Buhari

Ya ce kwanan nan wahalar karancin kudin za ta zama tarihi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa ba a kirkiro batun canjin kudi domin a karya kowa ba, kuma kwanan nan wahalar karancin kudin za ta wuce.

Buhari ya kuma ce gwamnatinsa za ta tabbatar ’yan kasa ba su cutu ba sanadiyyar canjin, yana mai ba da tabbacin cewa wahalar da ake sha a sakamakon hakan tana dab da wucewa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar.

Shugaban ya ce tun da farko ba don talakawa su sha wahala aka fito da shirin ba. Ya ce an fito da shi ne saboda maganin masu boye tsabar kudi a gida da rage yawan kudaden jabu da kuma rage ayyukan ta’addanci.

“Muna sane da cewa talakawa na cikin matsi sakamakon wannan batun, saboda sukan ajiye kudi a gida saboda bukatun yau da kullum, muna ba su tabbacin cewa ba za mu bar su su yi asara ba.

“Akwai nagartattun tsare-tsare da Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran bankunan kasuwanci suka fito da su domin gaggauta raba sabbin kudaden tare da yi duk mai yiwuwa wajen magance kalubalen da rashinsu yake haifar wa tattalin arzikin Najeriya.

A ranar 31 ga watan Janairun 2023 ne dai wa’adin da CBN ya diba na daina amfani da kudaden yake cika.

Sai dai har yanzu jama’a na ta tururuwar zuwa bankuna su kai kudaden nasu don gudun tafka asara, sannan kuma babu isassun sabbin takardun kudaden a hannun mutane.