✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba don jajircewar Buhari ba da matsalar tsaro ta fi haka muni —Ayade

Gwamnan Kuros Riba ya ce, kwarewa da kaifin basirar Shugaba Buhari sun taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade. ya ce da Najeriya ba ta samu jajirtacce kamar Shugaba Buhari ba, da matsalar tsaron kasar ta fi duk yadda ake zato tsanani.

Ayade, ya ce hakan ce ta sa zai bai wa bangaren tsaro muhimmanci fiye da kowanne  idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.

Ya ce, “Kwarewa da kaifin basira da kuma fahimtar sha’anin tsaro da Shugaba Buhari ke da su ya sa ya iya shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

“Ba don kokarinsa ba, da kasar nan ta fada cikin wani yanayi mafi muni, amma Buhari ya yi la’akari da halin da Afganistan ta fada da kuma yadda wasu mutane ke ganin cewa Yammacin Afrika mallakarsu ce, don haka suke ganin Musulmi da Kiristocin yankin ba su da addinin kwarai ya zama dole a shafe su.”

Ayade ya yi wadannan bayan ne a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi, ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

“Da a ce ba Muhammadu Buhari ne Shugaban Kasa ba, da abubuwa sun tabarbare; ina wannan magana ne da kwarin gwiwa, saboda na tuna yadda a baya ake samun tashin bama-bamai har a cikin Abuja

“An an yi nasarar sauke tutocin Boko Haram da suka karade wawsu jihohin Arewa duk da cewa hakan bai hana samun ’yan hare-hare nan da can ba.

“Shi yakin sunkuru abu ne da kan dauki tsawon shekara 30 zuwa 40; abin da ya faru da kasar Algeria shi ne misali mafi kusa da za mu iya tunawa.

“Hakika, faduwar Kasar Afghanistan ya zama babbar barazana ga tsaron kasa musamman kuma a yankin Arewa, inda mayakan ISWAP suka bayyana da aniyarsu karbe ikon yankin Afrika ta Yamma,” inji Mista Ayade.

A cewarsa, rashin ingantaccen tsari ya sa aka wayi gari shehunnan boko na barin jami’o’i suna shiga takara don a zabe su a mukamai daban-daban.