Mataimakin Daraktan Sadarwa na Majalisar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya ce ba don Buhari ne ke mulkar kasar ba, da tuni ta wargaje.
Lanre ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ranar Talata, inda ya ce ’yan kasar na hakuri ne da halin da ake ciki, kasancewar sun aminta da jagorancin jam’iyar APC.
A cewarsa, “Zan iya fada muku da kwarin guiwa cewa; ba don Buhari ne ke mulki ba, da tuni kasar nan ta durkushe.
“Dalili shi ne zamanin mulkin PDP, sojoji guduwa suke yi daga iyakokin Najeriya, saboda ba su da makaman yaki da masu kawo musu hari.
“Amincewa na tafiya ne kafada da kafada da hakuri, don haka akwai yarda tsakanin ‘yan Najeriya da Buhari tsawon shekara bakwai, saboda gwamnatin ta taka rawar gani a mulkinta.
“Sannan kuma suna ganin yadda ya ceto kasar a lokacin da suka yanke kauna da samun wanda zai yi hakan,” inji shi.