Babban Hafsan Tsaron Najeriya (CDS), Janar Lucky Irabor, ya ce suna fama da matsin lamba daga gurbatattun ’yan siyasa don hada kai da su a yi magudin zabe.
Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Najeriya Ta Fi Ko’ina Yawan Yara Masu HIV Da Tarin Fuka —WHO
- Sanatan PDP na yi wa Tinubu yakin neman zabe
Da yake amsa tambayar manema labarai, Irabor ya ce, tabbas, ba iya sojoji kadai ba, dukkanin jami’an tsaron Najeriya na fuskanatar wannan matsi daga kowane bangare.
“Ba iya mu ba ma, duk jami’an tsaro, na fuskantar haka idan zabe ya gabato, kuma haka duniyar marasa gaskiya take duk da suna sane da cewa ba daidai ba ne.
“Bambancin shi ne amfani da kwararru don tunkarar wadannan batutuwa, kuma abin da sojoji suka kuduri aniyar yi ke nan.”
“Shi ya sa ma muka zage damtse wajen shirya bitoci don wayar da kan jama’a, da kuma samun gyara kan haka,” in ji Irabor.
Da haka ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ba wa sojin Najeriya hadin kai, don ganin sun jajirce wajen ganin an gudanar da ingantaccen zabe lafiya a 2023.