✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kama Mata Masu Sayen Katinan Zabe a Kano

Kotu ta dage shari'ar matan da ake zargi da sayen katinan zabe zuwa watan Nuwambar 2023

Wata Kotu a Kano, ta gurfanar da wasu mata hudu da ake zargi da sayen katinan zabe a hannun mutane.

Dan Sanda mai gabatar da kara ya bayyana kotu cewa an kamo matan ne a unguwar Kadawa da ke Karamar Hukumar Ungoggo, kan laifin hada baki da sayen katinan zaben, wanda laifi ne karkshin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Bayan karanto musu tuhume-tuhumen da ake musu, matan sun musanta zargin, kuma alkalin kotun Mai Shari’a Faruk Ibrahim ya ba da belin su, da sharadin kowaccensu ta gabatar wa kotun wanda zai tsaya mata, da ya mallaki Naira miliyan daya.

Daga nan ne ya sanya ranar 6 ga watan Nuwambar 2023, don gabatar da shaidu.