✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba dole bane sai na fara wasa da Ozil- Arsene Wenger

Mai horar da qungiyar wasan qwallon qafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce a yanzu Mesut Ozil bai da tabbattacen waje a cikin ‘yan wasa…

Mai horar da qungiyar wasan qwallon qafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce a yanzu Mesut Ozil bai da tabbattacen waje a cikin ‘yan wasa 11 da za a fara wasa da su.

A cewar Wenger “Yana da amfani, amma muna da wasu ‘yan wasa irin su Jack Wilshere da Alex Iwobi. Dukansu za su iya buga abin da Ozil zai buga.

“Yanzu shi ma ya qara dagewa sosai. Kuma yana qoqari matuqa.

An daxe dai ana ta kai-komo a kan Ozil, inda xan wasan ya qi amincewa ya sabunta kwantiraginsa da qungiyar Arsenal, wanda hakan ya sa mai horar da qungiyar yake tunanin lokaci ya yi da za su raba gari da shi da abokin wasansa Alexis Sanches.