✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba dan kungiyarmu Hisbah ta kama ba a Kano —PSN

Kungiyar ta nesanta kanta da wanda hukumar Hisbah ta cafke.

Kungiyar Masu Hada Magunguna ta Najeriya (PSN) ta ce mutumin nan da Hukumar Hisbah ta cafke a Kano kan zargin cin zarafin wata mata ba dan kungiyar ba ne.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Mista Sani Ali ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi.

  1. ‘Yadda rawar da na taka a fim ta jawo min zagi a gari’
  2. Hushpuppi: An dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin dan sanda

“Mun damu matuka da rahoton da ke yawo na cewa an kama wani dan kungiyarmu.

“Nan da nan muka tunkari Hisbah don gano hakikanin wanda suka kama, inda aka sanar da mu cewa wanda aka kama ba likitan magani ba ne.

“Mutum ne wanda ya mallaki kantin sayar da magani na yau da kullum kuma ya ke kiran kansa kwararre.

“Muna son jama’a su lura cewa wanda aka kama ba kwararren masanin magunguna ba ne sabanin yadda wasu kafafen yada labarai na Intanet suka ruwaito.

“Manufarmu ita ce kore zargin da ake yi na cewa wanda aka kama dan kungiyarmu ne,” in ji shi.

Shugaban ya bayyana a fili cewa akwai banbanci tsakanin mai siyar da miyagun kwayoyi wanda ke da shago da kwararre ta fuskar sanin magunguna da Turance ake kira ‘Pharmacist’.

A bayan nan Hukumar Hisbah ta Kano, ta sanar da cafke wani mai sayar da miyagun kwayoyi a Gnguwar Sabuwar Gandu da ke kwaryar birnin Kano a bisa zargin cin zarafin wata mata.

%d bloggers like this: