✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba da yawu na aka zagi Buhari ba —Oba na Benin

Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya nesanta kansa da zagin Shugaba Buhari a shafukan zumunta tare da wasu mutum biyu da ya ce jihar…

Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya nesanta kansa da zagin Shugaba Buhari a shafukan zumunta tare da wasu mutum biyu da ya ce jihar Edo na alfahari da su.

Basaraken ya ce bai lamunce wa kowa zagin Buhari ko tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole ko Kyaftin Hosa Okubor ba, abin da ya kira da aikin masu neman magana.

“Muna allawadai da babbar murya game da cinn mutunci da aka yi wa Shugaba Buhari da sauran mutanen da bidiyon ya ambata”, inji Masarautar Benin.

Basaraken na martani ne ga wani bidiyo a shafukan zumunta, wanda a ciki wani mai suna Eranomigho Edegbe, ya ce Oban ya ba shi izini zagin Buhari da mutanen.

Obar Ewuare II, ya bukaci Eranomigho da ya nemi afuwarsa daga mummuan aikin da ya yi da ya zubar da kimar Masarautar ta Benin.

Sanarwar da Sakataren Majalisar Masarautar, Frank Irabor, ya fitar ta ce alakar basaraken da Shugaba Buhari dadaddiya ce, tun Buharin na shugaban hukumar PTF.

“Oba na Benin na jaddadawa cewa babu umurninsa ko amincewarsa a wannan bidiyo”, inji sanarwar.

Sanarwar ta ambaci Oshiomhole da Okunbur da cewa suna mutunta masarautar sun kuma ba da gudunmuwa wajen mata cigaba.