Tsohon wakilin Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar ƙalubalen tsaro a Arewacin Nijeriya ya fi ƙamari a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, fiye da lokacin shugaba Bola Tinubu a yanzu.
Sani, ya yi waɗannan kalamai ne a yayin bikin cika shekara 40 da ƙungiyar tsoffin ɗalibai ta Kagara ta yi.
- Yadda tirelar shanu ta faɗo daga saman gada a Kano
- MURIC da FOMWAN sun nemi a hukunta faston da ya raunata liman da iyalansa
An gudanar da bikin ne a makarantar sakandare ta Ahmadu Bahago da ke birnin Minna a Jihar Neja.
Ya jaddada buƙatar gwamnati ta jajirce wajen magance matsalolin tsaro, domin kaucewa kurakuran da gwamnatin baya ta yi.
Sani, ya ce makarantu da cibiyoyin ilimi a lokacin da Buhari sun fuskanci munanan hare-hare, inda ’yan bindiga ke yi wa ɗalibai ɗauki ɗai-ɗai.
A cewarsa makarantu irin su Jami’ar Green Field da Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati ta Kagara, da sauransu sun fuskanci hare-haren ‘yan fashin daji.
Ya yaba wa gwamnati mai ci bisa ƙoƙarin da ta ke yi wajen kawar da manyan ‘yan ta’adda tare da yi wa gwamnatin fatan samun ci gaba.
Sani ya kuma goyi bayan gwamnatin Jihar Neja na ɗauki Kwalejin Kagara, amma ya buƙaci sake buɗe makarantar, bayan ingantar tsaro a yankin.
Ja’afar Tukur, shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Kagara, kuma mataimakin Kwamanda a hukumar Kwastam, wanda Dokta Philip Audu Ibrahim ya wakilta, ya nuna rashin jin daɗinsa kan halin da makarantar ke ciki.
Ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su magance ayyukan ’yan tada ƙayar baya.
Kwalejin Kimiyya ta Kagara an rufe ta tun 2021 tare da mayar shingen sojoji biyo bayan harin ’yan bindiga wanda suka sace ɗalibai da malamai a makarantar.