✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba Bahuri ya kawo wahalar da ake ciki ba – Akibishop Kaigama

Akibishop na darikar Katolika da ke Jos kuma Shugaban Bishop-Bishop din cocin Katiolika na Najeriya Akibishop Ignatius Kaigama, ya ce ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari…

Akibishop na darikar Katolika da ke Jos kuma Shugaban Bishop-Bishop din cocin Katiolika na Najeriya Akibishop Ignatius Kaigama, ya ce ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kawo wahalar da ake ciki a Najeriya ba, kamar yadda wasu suke dora masa.
Akibishop Ignatius Kaigama ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce “Babu shakka mutane suna cikin wahala a Najeriya, amma ya kamata mu fahimci cewa abubuwa sun dade da baci a kasar nan. Don haka bai kamata mu dora wa Shugaban kasa ba.”
Ya ce na farko man fetur da muka dogara da shi yanzu farashinsa ya fadi a duniya. Ya ce “A da mun manta da aikin noma da harkokin kasuwanci da ma’adanai. Mun dogara da man fetur ne kawai, kowa yana neman babban aikin gwamnati, ba wanda yake son ya yi aikin wahala.”
Akibishop Kaigama ya ce saboda faduwar man fetur da muka dogara da shi, ya sanya yanzu gwamnatocin jihohin kasar nan ba su samun kudin da ya kamata su biya albashin ma’aikatansu.
Ya ce ita kanta Gwamnatin Tarayya akwai ayyuka da dama a kanta kamar maganar tsaro wanda yake kusan cinye duk kudin da take samu, domin maganar yaki da Boko Haram da ’yan tawayen Neja-Delta ba karamin abu bane. Don haka dole gwamnati ta sanya kudi a aikin soja da ’yan sanda da sauran bangarorin tsaro.
“Ya kamata ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu su nemi hanyoyin da za a gyara wadannan matsaloli, maimakon a dora wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Mu bayar da shawarwari masu kyau kan yadda za a gyara wadannan matsaloli, kuma masu mugun halin da suke cikinmu su gyara halayensu, masu cin hanci da rashawa da satar kudin jama’a su daina,” inji shi.