✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a zargin mai Shari’a Bulkachuwa da laifin cin hanci da rashawa

Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata zargin cewar mai shari’a Zainab Bulkachuwa, shugabar kotun sauraren karar zaben Shugaban Kasa tana da hannu wajen…

Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata zargin cewar mai shari’a Zainab Bulkachuwa, shugabar kotun sauraren karar zaben Shugaban Kasa tana da hannu wajen zargin cin hanci da rashawa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mista Peter Adunanya shi ne ya bayyana hakan a Abuja, inda yake maida martani akan zargin cewar wai hukumarsu tana bincike a kanta, ya ce wannan zargi shirme ne kawai, bashi da tushe, sai yayi kira ga alumma dasu guji yada labaran da ba su da sahihanci don bata wa wani suna.

Adunanya ya kuma bayyana wannan rahoto da cewar abin takaici ne, ya ce hukumar tuni ta fara gudanar da bincike akan lamarin, sai ya shawarci ‘yan siyasa da su kasance masu bin dokokin shari’a, su kyale hukumar ta yi aikinta, ya ce hukumarsu za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da kafofin yada labarai a matsayinsu na masu kawo ci gaban kasa.

Hakazalika ya gargadi masu yada jita jita dasu guji yin hakan, domin duk wanda ya shiga hannu to, zai fuskanci fushin hukuma.ya ce hukumar ba za ta gaza ba, wajen sauke nauyin da ke wuyan ta na ba da dama ga ‘yan kasa na gari masu bin doka damar aiwatar da abin da bai sabawa shari’a ba.

“Cin zarafin alkalai ko yi musu kazafi, kawai don hukuncin da aka yanke bai yi maka dadi ba, amma idan abin ya yi maka dadi ba a jin bakin ka. Yace jamiyar PDP akan sakamakon zaben Gwamnan jihar Osun tayi musu dadi, amma sai gashi yanzu fara hargowa domin basu sami nasara ba a kotun daukaka kara.Ya ce idan har PDP za ta ci gaba da bata sunan masu shari’a ta labaran karya, ya ce lallale zamu samu kanmu cikin wani hali da Alkalai za su rinka jin tsoron aiwatar da shari’oin dake hannunsu, wanda hakan kan iya kawo jinkiri wajen yanke hukunci.”