Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta karyata labarin da ke yawo cewa kungiyar Boko Haram da ’yan bindiga sun kai hari a mahaifar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, shi ne ya karya labarin da aka yada cewa mahara sun kai hari kan mazauna kauyukan da ke yanin Dugwaba a Karamar Hukumar Hong ta jihar.
- ’Yan bindiga sun kwace iko da ‘garin’ su Boss Mustapha
- Mota cike da fasinjoji ta fada katuwar kwata a Legas
Nguroje ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) cewa rundunar ’yan sandan jihar ta aike da tawaga ta musamman yankin don tabbatar da tsaro.
Ya ce ya zuwa yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaron da aka aike zuwa yankin da ke nuni da cewa an kai hari.
“Mun samu rahoto cewa mutane suna barin kauyukansu sakamakon harin Boko Haram.
“A matsayinmu na jami’an tsaro ba ma wasa da duk wani bayani da ya shafi harkar tsaro.
“Tuni aka aike da tawagar yaki da ta’addanci zuwa yankin, kuma har yanzu ba mu samu rahoton wani hari ko farmaki da aka kai,” kamar yadda ya shaida wa NAN.
Shi ma Hakimin Gundumar Dugwaba, Mista Simon Yakubu, ya karyata labarin harin, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne.
Yakubu ya ce jama’ar yankin na kunciyar hankali kuma suna cikin gudanar da bukukuwan Kirsimeti ne aka fitar da rahoton karyan.
“Babu gaskiya a cikin labarin, sannan ba komai zai haifar ba face rudani a tsakanin mazauna yankin nan.
“Duk wanda ya fitar da labarin karyan ba mai son zaman lafiya da ci gaba ba ne a tsakanin al’umma,” inji Yakubu.
Ya ce ya samu labarin tabbacin mutanen kauyukan na ci gaba da hada-hadar kasuwancinsu kamar yadda suka saba.