✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a fahimci jawabin Shugaba Buhari game da matasa ba – Wazirin Kasuwar Alaba Rago

A daidai lokacin da al’ummar kasar nan ke tofa albarkacin bakin su bisa kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matasan Najeriya, Alhaji Adamu Katagum, Wazirin…

A daidai lokacin da al’ummar kasar nan ke tofa albarkacin bakin su bisa kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matasan Najeriya, Alhaji Adamu Katagum, Wazirin Sarkin Kasuwar Alaba Rago kana kuma shugaban gidauniyar talakawa ya shaida wa Aminiya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kyakyawar manufa akan matasan kasar nan. 

Ya ce duk da kasancewar Shugaba Buhari kusan shi kadai ne ke kokarin ganin abubuwa sun tafi yadda ake so, “domin hausawa sun ce hannu daya ba ya daukar jinka, idan ka dubi ma’aikata da sauran masu madafun iko da za ka kasa su gida dari da kyar zaka sami kaso goma masu manufar gyara kasa irin shugaba Buhari, don haka addu’oin da talakawa suka yi a baya ya zama wajibi su cigaba har Allah Ya bai wa Shugaba Buhari mataimaka nagari, amma idan ka lura da irin aikin gyara da ya dauko zaka yadda da cewa Buhari na da kyawawan tanadi ga matasan kasar nan,  tun daga fannin samar da tsaro domin cigaban harkokin kasa na yau da kullum, bunkasar harkokin noma da kiwo domin a yanzu dubban matasanmu sun koma noma, shirin nan na N-power ya taimakawa dubban matasan kasar nan, don haka maganar nan da ya yi ai ya yi ne bada mumnunar manufa ba sai don gyara da karawa matasan kaimi,” in ji shi.

Alhaji Nura Adamu Katagum ya yi kira ga gwamnonin jihohin da ake cigaba da samu tashin-tashana irin su jihohin Zamfara da Taraba da Benuwai da su yi hubbasar magance matsalar, “domin hakkin wadannan gwamnonin ne su tabbatar an sami zaman lafiya a jihohin su don sun fi kowa sanin duk abin da ke faruwa da ma batagarin da suke tada hankulan jama’ar su,  don haka suma ya kamata su yi hubbasa kamar yadda shugaba Buhari ya yi, mu kuma za mu cigaba da yin addu’a don ganin wannan gwamnati da Allah ya bamu ta cinmma nasara,” a cewarsa. 

Ya ce idan shugaba ya yi nasarar dare wa karagar mulki a shekarar 2019 za a amfana da kyawawan ayyukan da ya dauko kuma matasa ne za su fi kowa cin moriyar hakan.