Tubabben Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce shi bai yi murna da mutuwar Shugaban Ma’aikatan a Fadar Shugaban Kasa Malam Abba Kyari ba.
Da yake bayyana hakan a wata sanarwa, tsohon kwamishinan ya ce a matsayinsa na Musulmi kuma mai kishin Najeriya, wadanda suka zaci ya yi murna da mutuwar Malam Abba Kyari ne ba su fahimce shi ba.
“Na wallafa sakwanni da dama a Facebook din da kuma ta hannun mataimakana na musamman ina alhinin mutuwar Abba Kyari, amma babu wanda ya yaba ko ya yi ikirari cewa na yi.
“A maimakon haka sai jama’a suka dira a kan wadansu kalmomi da aka yiwa mummunar fassara da nufin bata min suna a matsayina na kwamishina a Gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje kuma mai goyon bayanshi sau da kafa…” inji shi.
- An tube kwamishina a Kano don murnar rasuwar Abba Kyari
- Abba Kyari na cikin nagartattun ’yan Najeriya —Buhari
Ya kara da cewa ya yi amfani da kalmomin win win ne a yunkurinsa na fayyace matsayin Muslunci game da mutanen da suka rasa rayukansu a annoba.
A cewarsa, Malam Abba Kyari ya yi dace COVID-19 ta yi ajalinsa, saboda ya yi shahada kamar yadda karantarwar Musulunci ta nuna.
“Manzonmu (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya tabbatar mana da hanyoyin shahada a Sahihul Bukhari, Kitabul Jihad was Siyar.
“Hatta Shaikh Isa Ali Pantami ya dauki lokaci yana bayani a kan wannan. Ke nan rasuwar Malam Abba Kyari babbar nasara ce a gare shi, wadda kusan burin ko wane Musulmi ke nan”, inji tubabben kwamishinan.
Daga nan sai ya nemi yafiyar iyalan marigayin da Gwamna Ganduje sakamakon bacin ran da ya haddasa musu bisa kuskure.