Gwamnatin Jihar Gombe ta ce har yanzu ba a ba ta shinkafar tallafi da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jihohi alƙawari ba.
Mai magana da yawun gwamnatun jihar, Ismaila Uba Misilli, ne ya munsata iƙirarin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, na cewa jihar ta karɓi tireloli 20 na shinkafar tallafin da Tunubu ya yi alkwari domin rage wa talakawa raɗaɗin yunwa da tsadar rayuwa.
Ismaila Uba Misilli, ya tabbatar da cewa kawo yanzu, sanarwar ware musu shinkafar ce kawai aka yi, amma ba a kai ga ba wa Jihar Gombe ba.
Ya ƙara da cewa, a iya saninsa, jihohi maƙwabtan Gombe a yankin Arewa maso Gabas irin su Adamawa, Yobe, Taraba, su ma ba a ba su masu shinkafar ta tallafi ba.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Siyan Hannun Jari A Banki
- Mutum 5 sun mutu wasu sun ɓace a kifewar kwale-kwale a Jigawa
Daraktan yaɗa labaran, ya buƙaci ministan ya fito ya yi ƙarin bayani kan maganar ba wa Gombe kasonta na shinkafar tallafin domin kawar da zargi.
A ƙarshe ya buƙaci ministan ya tantance gaskiyar iƙirarin da ya yi, da kuma gano haƙiƙanin inda shinkafar ta maƙale.
A ƙarshe ya yi fatan nan ba da jimawa ba za a ba wa Jihar Gombe nata shinkafar tallafin domin raba wa talakawanta.