✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baƙuwar cuta ta kashe mutum 11, an kwantar da 30 a Gombe

Cutar ta kwantar da mutum 30, yayin da aka sallami 50 daga asibiti.

Wata baƙuwar cuta ta ɓulla a ƙauyen Chessi da ke gundumar Kulani a yankin ƙaramar hukumar Balanga, inda ta kashe mutum 11 tare da kwantar wasu 30 a asibiti.

Kazalika an sallami mutum 50 daga asibiti.

Tawagar likitocin da suka haɗa da Dokta Esrael James da Yakubu Ishaya Maina, sun fayyace cewa cutar ba kwalara ba ce amma sun ɗauki samfurin jini da ruwa na waɗanda suka kamu da cutar don gudanar da gwaji.

Sun bayyana cewar mutum 30 na kwance a asibiti, inda cutar ke da alamun ciwon kai, zazzabi, ciwon ido da kuma ciwon ciki.

Likitocin sun shawarci al’umma da su kai rahoton duk wasu alamun cutar da ake zargi ga cibiyar lafiya da aka kafa a makarantar firamare ta garin Chessi.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Balanga ta Arewa, a majalisar dokokin jihar, Musa Buba, ya bayar da tallafin magunguna da kayayyakin masarufi na sama da miliyan 1.5 ga al’ummar yankin Chessi.

Buba, ya ce ya bayar da wannan tallafi ne a lokacin da ya ji rahoton ɓullar cutar, ya kuma ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa aikewa da tawaga daga ma’aikatar lafiya da kuma cibiyar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC).

Hakimin Kulani Alhaji Umaru Alhaji, ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da kuma ɗan majalisar kan ba su tallafi.

Wasu daga cikin marasa lafiyar, Habiba Salisu da Aisha Mohammed da Mohammed Sulaiman sun nuna godiyarsu ga ɗan majalisar na samar musu da magunguna da kayan masarufi.