✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azzaluman duniya sun doshi tarwatsa Najeriya (2)

A yau kuma za mu tuna baya ne, domin kuwa wannan tsokaci mai take na sama, na taba kawo shi nan a cikin 2011, shekaru…

Yadda harin bam din ’yan Boko Haram ya tarwatsa dukiya a Kano, Lahadin da ta gabataA yau kuma za mu tuna baya ne, domin kuwa wannan tsokaci mai take na sama, na taba kawo shi nan a cikin 2011, shekaru uku da suka gabata. Idan aka yi nazarinsa, za a fahimci dalilin da ya sanya na sake maido shi, domin mu tuna baya, wanda Hausawa suka ce shi ne roko. Ga karashen tsokacin nan, kamar yadda yake:
***
Ko me ya ja hankalin Bature Gordon Duff har ya ga cewa ya kamata ya ankarar da al’ummar Najeriya da shugabanninta? Ga dalilinsa: “Ba ina rubuta wannan makala ba ne a matsayina na dan jarida. Ni sananne ne a Najeriya, a matsayin kwararren masani ta fuskar harkokin tsaro, wanda ya dade a wannan fage. Ina da manyan abokai, wadanda suka kasance shugabanni a gwamnatin wannan kasa. Don haka, na rubuta wannan jan hankali ne kawai saboda kaunar musamman da nake wa kasar.”
Ya nuna cewa babban dalilin da ya sanya azzaluman nan suke son ganin cewa sun wargaza Najeriya shi ne, saboda ita tafi yawan al’umma a Afrika, mai dimbin arziki. Idan aka kyale kasar ta zauna lafiya, za ta iya samun bunkasa da ci gaba, sannan ta zama barazana ga manyan azzaluman kasashe. Dalili ke nan ya ce wadannan muggan mutane suka hada kai da wasu hamshakan ’yan siyasa da wasu manyan shugabannin hukumomin tsaro, suka assasa kafa karkatattun kungiyoyi, irin Boko Haramun, domin su cin ma burinsu.
Ya kara da cewa, matakan da suke dauka shi ne, na farko za su tabbatar da cewa shugaban da ke kan mulki bai samu karfin halin aiwatar da wani abin kirki ga al’umma ba. Za su yada tsoro da rashin yarda tsakanin al’umma. Dalili ke nan ma suke dasa bama-bamai a coci-coci, wanda haka zai sanya a haddasa babbar gaba tsakanin mabiya manyan addinan kasar guda biyu, wato Musulunci da Kiristanci. Idan an samu nasarar haka, shi ke nan sai yakin basasa ya balle tsakanin Musulmi da Kirista ko kuma tsakanin Arewa da Kudu. Daga nan babu abin da zai biyo baya sai tarwatsewar Najeriya.
Wannan hasashe na da kamshin gaskiya, domin kuwa mutum zai yi tambayar cewa, me ya sanya lokacin da aka kama Muhammad Yusuf da ransa, sai wasu jam’an tsaro suka yi saurin kashe shi, ba tare da an yi wani bincike ba? Wannan na nuna cewa da an kyale shi, zai iya tona asirin wasu bara-gurbin manya da ke daure wa ta’addacin gindi. Haka kuma, lokacin da aka taba gurfanar da su Muhammad Yusuf a wata kotun Abuja, tun a shekarun tsakanin 2003 zuwa 2004, wasu hamshakan ’yan siyasa ne suka amshi belinsu, duk da cewa su ba Musulmi ba ne kuma a zahiri ba su da wata alaka da su. Haka kuma, akwai wanda ya tabbatar mani da cewa marigayi Shaikh Jafar Adam, an halaka shi ne a sanadiyyar ya ce zai tona asirin wasu hamshakan mutane da suka amso kwangilar wargaza Najeriya.
Ya ku al’ummar Najeriya – Yarabawa, Hausawa, Inyamurai, Tibi, Nufawa, Fulani, Jukunawa, Ibibiyo, Itsekiri, Angas da dukkan kowace kabila, mu shafa wa kanmu lafiya. Mu kunyata azzaluman duniya, mu zauna lafiya da juna. Ya ku mabiya manyan addinai, Musulmi da Kirista, mu duba koyarwar annabawanmu masu daraja, mu kaunaci juna, mu ba mabiya shaidan kunya. Mu zauna lafiya da juna. Mu gane cewa sai muna da rai ne za mu tsinana abin kirki. Mu fahimta da cewa sai muna zaune lafiya ne za mu bunkasa mu ci gaba. Mu ci gaba da addu’a, Allah Ya karya mugun nufin Shaidan, Allah Ya wargaza bakar aniyar azzaluman duniya. Allah Ya sanya Najeriya ta dore a matsayin kasa daya al’umma daya. Allah Ya gyara zukatan karkatattun matasanmu da karkatattun shugabanninmu, su zama nakwarai. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da bunkasar arziki. Amin!

Budaddiyar Wasika Daga ’Yan Acaba Ga Gwamnan Kaduna

Aliyu danlabaran Zariya (08050205757), rigar ’yan acaba ya shiga, ya rubuta wa Gwamnan Jihar Kaduna wasika, kamar haka:
Ranka shi dade, bayan dubun gaisuwa tare da fatan kana lafiya.
Tun lokacin da muka ji cewa ’yan majalisarka sun kawo kudurin hana mu sana’ar da muke yi don neman na sanyawa a bakin salati, a daidai lokacin ne mafiya yawa daga cikinmu hantarmu ta kada; domin kuwa wannan dokar ba mu kadai za ta shafa ba. Sana’ar acaba wata masana’anta ce mai zaman kanta, inda ta tattara al’umma kala-kala. Na farko akwai masu sayar da kayan gyara, ga masu sayar da abinci, ga masu sana’ar kanikanci, ga masu gyaran taya, ga masu wanke babura, ga uwa uba yaran da ake kai wa makaranta da safe. Hakika abin na da yawa, sai dai kawai mu takaita, don kar mu jawo wa wasu hawan jini.
Akalla mu masu wannan sana’ar mun haura miliyan daya, sai ga shi an kawo wa jihar Keke-Napep din da bai wuce 750 ba, wanda ko keke daya za a bai wa mutum 50 ba zai isa ba.
Mun dade muna maka fatan alheri. Na tuna da lokacin da ka hau karagar mulki, bayan marigayi Sir. Patrick Ibrahim Yakowa, mu din nan ne muka yi dandazo muka dinga wasa da Babura, muna taya ka murna amma daga karshe ga abin da za ka saka mana das hi! Na baya-bayan nan ma lokacin da aka nada ka Dallatu, ba mu yi kasa a gwiwa ba; muka dinga murza babura don dai kawai soyayyar da muke maka amma ashe kai ba hakan take ba a bangarenka. Hakika ba wai muna ja da dokar ba ne, a’a, muna ja da hanyar da aka bi aka yi dokar ne.
Ya mai girma Gwamna, hakika tun lokacin da wannan sana’a ta fara fitowa, wato a Jamhuriya ta biyu, zamanin mulkin Shagari, ba wani abu ya sa hakan ba sai talauci a wancan lokaci amma a zamanin yau, akwai talaucin akwai kuma rashin aikin yi, don hatta masu Diploma, akwai su a wannan sana’ar, ban da masu kananan albashi da suke kara yawa; don dai a sami zaman lafiya cikin iyalai. Kuma mu ’yan acaba mutane ne masu bin doka da oda, don hatta gwamnati ta san da hakan. Duk mahada-mahada da ake biyan haraji, muna biya kuma gwamnati na samun kudin shiga.
Ta bangarenmu kuwa, a cikinmu akwai wadanda ba su da wata sana’a sai sayar da wiwi, kwaya da kuma sace-sace amma cikin ikon Allah wannan sana’a ta yi masu saiti, har idonsu ya bude suka iya neman halas dinsu komin ruwa ko zafi. Kamata ya yi daga lokacin da aka sanya wa wannan doka hannu, a sanya mana isasshen lokaci daga wata shida ko shekara guda, yadda wasunmu za su kimtsa su canza sana’a ko kuma su yi tattalin neman na Keke Napep kafin lokacin amma kawai sai a ka yi mana hukuncin gaggawa, wanda kuma dimokuradiyya muke. Ya kamata a mutunta mu a matsayin mu na ’yan kasa masu daraja.
Ya maigirma Gwamna, hakika akwai azzalumai masu janyo maka magana cikin tafiyarka, mun san kai mutumin kirki ne amma cikin mashawartanka da ’yan majalisarka akwai masu neman su janyo maka bakin jini, musamman yadda suke fitowa kafafen yada labarai suna rigima da al’umma, ga shi suna sanya wata katanga a tsakaninka da al’ummar da kake mulka, ga haddasa gaba da suke yi a tsakaninka da al’umma. Don haka ya kamata ka yi karatun ta-natsu tun kafin su kai ka su baro.
Kar in yi tuya in manta da albasa, hakika wannan bahaguwar dokar hatta jama’ar gari sun yi Allah wadai da ita. Guragu, mata, yara duk sun yi Allah wadai, don kuwa ba a kawo musu makwafin baburan ba, don Keke Napep ba dukkan sako da lungu za su shiga ba, akwai ma lungun da ya yi kankanta, musamman a cikin garin Zariya, inda sai dai babur kadai zai iya shiga.
Mu ’yan acaba muna maka fatan alheri. Yadda ka yi mana idan kana ganin gyara ne, muna rokon Allah Ya yi maka irin yadda ka yii mana, musamman a zaben 2015 mai zuwa.

Hidindimun Gizagawa Na Wannan Makon

A labarin farin ciki, mun samu sako daga daya daga cikin iyayen Gizagawan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Zakari (Zanwan Lafiya), Hakimin Gundumar Zanwa (08096430960), wanda ya ce: “Assalamu alaikum, gaisuwa da fatan alheri ga wannan fili da daukacin Gizagawan Zumunci. A madadin ni da iyalina da jama’ar gundumar Zanwa, muna  farin cikin taya mai martaba Sarkin Lafiyar Bare-Bari, Alhaji (Dokta) Isa Mustafa Agwai 1 (CFR) murnar cika shekara 40 a gadon sarauta. Allah Ya ja zamanin sarki, Ya kara masa lafiya, kwanciyar hankali da masarautar Lafiya baki daya.”
Muna taya mai martaba murna, Allah kara yawancin kwana da rabo mai amfani. Amin! – Gizago.