✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azzaluman duniya sun doshi tarwatsa Najeriya (1)

A yau kuma za mu tuna baya ne, domin kuwa wannan tsokaci mai take na sama, na taba kawo shi nan a cikin 2011, shekaru…

A yau kuma za mu tuna baya ne, domin kuwa wannan tsokaci mai take na sama, na taba kawo shi nan a cikin 2011, shekaru uku da suka gabata. Idan aka yi nazarinsa, za a fahimci dalilin da ya sanya na sake maido shi, domin mu tuna baya, wanda Hausawa suka ce shi ne roko. Ga tsokacin, kamar yadda yake:
***
Tare da alhini da takaici nake bude wannan tsokaci mai take na sama. Tun ma kafin in gabatar da maudu’in wannan tsokaci, duk wani da ya kwana kuma ya tashi, zai iya kirdadon abin da ya saka ni cikin takaici da alhini, musamman ganin cewa tatsuniyar gizo dai ba za ta wuce koki ba. A takaice dai kowa ya san yadda Najeiya ta zama wani dandali na zubar da jinin talakawa, wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba. Tun daga Maiduguri zuwa Damaturu, hada da Bauchi da Jos; karo da Kaduna da wasu sassa na Jihar Naje, uwa uba, har ma da Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, kullum sai zubar da jini ake.
Har kullum tambayoyin da ke karakaina a kwakwalwar mabambantan mutane su ne, shin su wane ne ke samun farin ciki da nishadi wajen halaka al’umma? Su wane ne kanwa uwar gamin da ke haddasa wannan ta’addanci? Shin me ke manufarsu, da suka zabi su ruguza rayuwar mayawaitan al’ummar kasar nan? Shin ta ina suke samun wadannan bama-bamai masu tsananin karfi, da har suke cin ma wannan karkatattar manufa tasu? Ya zama dole ga mutane da suke tofa wadannan mabambantan tambayoyi, domin kuwa barnar ta yi yawa.
Domin neman gamsassun amsoshin wadannan tambayoyi, masu tunani sun yi, masu hasashe sun yi, haka ma masu ba da amsa kai tsaye sun ba da amma duk da haka, har yanzu abin bai gamsar ba, ganin cewa har yanzu ta’annatin sai kara afkuwa yake. Jami’an tsaro kuwa sai suka kasance cikin tsoro da kara haddasa tsoro ga al’umma, maimakon su ba da kariya da tsaro, kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Bari mu duba amsa ta farko, wadda ke ta’allaka wannan ta’annati ga dakarun Boko Haramun. Wannan kuwa a fili yake, musamman ganin cewa da zarar an samu tashin bam, musamman a Arewacin Najeriya, sai kakakin rundunar ya ba da sanarwar cewa kungiyarsu ce ke da ruwa a ciki. Idan muka fara lissafin tashin bama-bamai a Maiduguri da Damaturu da wanda ya faru a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja da wanda ya faru a ginin Majalisar dinkin Duniya da ke Abuja, da kuma wanda ya faru a Lahadin makon jiya a garin Madalla, duk kungiyar ce ta dauki alhakin faruwarsu.
Abin tambayar shi ne, to su wane ne ’yan Boko Haramun? Domin kuwa har yanzu babu wanda ya fito fili ya ce sunansa wane dan wane, kuma shi ne jagoran kungiyar. Tun bayan kisan gillar da aka yi wa shugabansu na farko, Muhammad Yusuf. Ke nan akwai yiwuwar cewa wasu ne ke fakewa da kungiyar suna son cin ma wata boyayyar manufarsu.
A wasu nazarce-nazarce da na gudanar, na ci karo da bayanai masu dimbin yawa, wadanda ke ba da amsa karara ga wannan abu da ke faruwa a Najeriya. A wannan nazari da na gudanar, na gano wadanda suke gudanar da wannan ta’annati da kuma wadanda suka daure gindi ake gudanar da shi. Ka fadi da ihu, ba wasu ne ba masu wannan karkatattar akida da mugun nufi sai azzaluman duniya. Game da abin da suke nufin cin mawa kuwa, na gano cewa babban burinsu shi ne, su tarwatsa Najeriya, ya zamanto nan gaba an share sunanta daga doron kasa. Za mu ga karin bayani nan gaba kadan.
A wani littafi mai suna ‘Dajjal: The AntiChrist’ wanda wani kwararren malamin Musulunci na duniya, Ahmad Thomson ya rubuta. Ya tona asirin makiya al’umma, makiya Musulunci, azzaluman duniya. Haka kuma ya kira su da sunan Masu Bautar Shaidan, wadanda ba su son ganin duk wata akida ko al’ada ta kirki tana gudana a duniya. Babu abin da suka sanya gaba sai duniya da bautar abin duniya. Domin cin ma manufarsu, za su iya yin duk wani abu komai muninsa, kama tun daga tsafi, kisan kai da sauransu.
Wadannan karkatattun mutane, masu siffar shaidanu, sun yi sansani ne a manyan kasashen duniya. Su ne ummul haba’isin duk wata ja’iba da ke faruwa a sassan duniya. Tashin-tashina da bala’o’in da ke addabar kasashen Musulmi, kamar su Irak, Pakistan, Libya, Siriya, Masar da Afganistan da sauransu, duk aika-aikar wadannan karkatattun azzaluman duniya ne.
Wani dalili da ya sanya na yanke hukuncin cewa wadannan azzalumai ne ke da alhakin tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Najeriya shi ne, a can baya, wani daga cikin jami’in wadannan azzaluman duniya, ya taba fitowa baro-baro ya tabbatar da cewa, Najeriya za ta wargaje, nan da shekarar 2015. Tun daga wannan lokaci abubuwa rikitattu suka yi ta faruwa, wadanda suka hada da tashe-tashen hankula masu yoyo da kabilanci, siyasa ko addini da sauransu.
Ban gama fahimtar haka ba, sai da na karanta wata makala da wani kwararren dan jarida na duniya, mai suna Gordon Duff ya rubuta, kuma aka wallafa ta a jaridar Daily Trust ta ranar Litinin da ta gabata, a shafi na 64. A makalar tasa, wacce ya yi wa taken: ‘An Durfafi Tarwatsa Najeriya’ kamar yadda ya ce, ya rubuta ta ne a matsayin gargadi ga shugabannin Najeriya domin su dauki matakan da suka dace, domin hana afkuwar wannan mugun kuduri na azzaluman duniya.
Za mu ci gaba
***

Hidindimun Gizagawa na wannan makon

Gyaran Rijista: A makon jiya mun yi kuskure wajen saka lambobin sababbin Gizagawan da aka yi wa rijista. Ga gyara nan:
1-R.S.M. N. Jibo, 08038962425 (GZG696LGS). 2-Lawal Adamu, 08056870486 (GZG697LGS). 3-Rabi’u Lawal D.T.M, 08034934325 (GZG698LGS). 4-Hamisu Maikyamis, 08068468445 (GZG699LGS). 5-Murjanatu Abu Sadik (GZG700LGS). 6-Nana Asama’u Alaba (GZG701LGS). 7-Sa’adiya Sabo (GZG702LGS). 8-Abdulkadir M. Gabas Ajingi Jihar Kano, 08066096105 (GZG703KNO). 9-Usman Abubakar kofar Kabuga Kano, 08035930617 (GZG704KNO). 10-Sulaiman Hussaini Ibrahim Haske, 08091221507 (GZG705KNO). 11-Hamisu Hamza Na’ibawa, 07035875470 (GZG706KNO). 12-Abdulganiyu Nabilisi, 08181730823 (GZG707KNO). 13-Hamza Fagge, 07057344990 (GZG708KNO). 14-Ladidi Ahmad Gwale, 08057115885 (GZG709KNO). 15-Lantana Rabiu Kurna, 08178070471 (GZG710KNO). 16-Buhari Hadi General,  07060806295 (GZG711KNO). 17-Injiniya Lukman Faragai, 08065461615 (GZG712KNO). 18-Auwalu Shehu dandodo, 08030435991 (GZG713KNO). 19-Bilyaminu Z. Ayagi, 07082460796 (GZG714KNO).