Hawaye na zuba a kan kuncinta, wata baiwar Allah da ke zaune a unguwar Umarari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta ce yayin da ake tashi da azumi, da ruwa ta yi sahur.
Ta bayyana hakan ne dai yayin da a ranar Juma’a ake shiga yini na biyu na dokar kulle a jihar Borno, kuma rana ta farko ta watan Ramadan na bana, ma’ana rana ta farko ta azumi.
Gwamnatin jihar ce dai ta ayyana dokar da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
Godiyar Allah
Yayin da Aminiya ke jin ta-bakin mazauna birnin Maiduguri a kan yadda suke yin azumi a halin zaman kulle, Ya Fannah Ali cewa ta yi ba ta da abin fadi, illa ta gode wa Allah da ya sa ta ga wannan wata na Ramadan.
“Amma a yi maganar wanne hali ake azumi? Ai ba ta ma taso ba, ka gan ni a zaune nan, ruwa kawai muka sha, a matsayin sahur, don ba mu da shi, kuma babu wanda ya kawo mana agajin ko sha kadai daya na shinkafa.
“Babu komai, akwai Allah”, inji ta sannan ta ci gaba da fada cikin hawaye, “An kulle mu, ba inda za mu je, don samo a bin sakawa a baki, to ai idan cutar ba ta hallaka mu ba, yunwa za ta hallaka mu.
“Ruwa nayi sahur da shi, kuma wallahi idan lokacin bude-baki ya yi, in ba Allah Ya kawo mana dauki ba, haka za mu sake shan ruwa mu hakura”, inji Ya Fannah.
Wannan abin takaici ne
Malam Juddum Usman ma cewa ya yi hakika wannan lamari abin takaici ne, to amma babu yadda mutum zai yi, sai hakuri ya mika wa Allah lamarinsa.
“Sannan akwai bukatar Gwamnati ta hanzarta daukar mataki don kada yunwa ta yi wa mutane kisan mummuke, mafi akasarin jama’armu ’yan gudun hijira ne, wadanda a kullum suna bukatar tallafi; babu kulle ma yaya muka karasa, balle ga kulle ga kuma azumi?
“Don haka ina kira ga Gwamna Babagana Umara Zulum da ya taimaka wa jama’a ta hanyar bayar da abinci don a samu saukin rayuwa”, inji Malam Juddum.
’Yan gudun hijira
Shi kuwa Kyari Ali kira ya yi da a dubi Allah, a tausaya wa jama’a “don muna cikin halin kaka-nika-yi—babu kulle ma yaya ta kare, abin da za a ci yana zama wahala?
“Kamar ni ina da ’ya’ya biyar da mace daya, kuma ni dan gudun hijira ne, daman sai ka fita za ka samu abin da za a ci, ga azumi, idan har fa, gwamnati ba ta kawo dauki ba, to yunwa za ta kashe mutane fiye da cutar coronavirus, don haka akwai bukatar a sake duba lamarin”, inji shi.
Shi kuwa Hussaini Adam cewa ya yi duk da an biya albashi tun ranar Juma’ar da ta gabata, a yanzu babu komai a hannu mutane, don kowa ya kwashe kudinsa ya sai abin da zai ci da iyalansa.
“Gaskiya lamarin bai yi dadi ba, tun da a lokutan azumi da babu kulle, ko almajiri sai ya samu abinci ya bari, amma a yau kowa na hannu-baka-hannu-kwarya, kai ma bai isheka ba, balle ka bayar”.
Sai ya yi kira ga gwamnati ta sassauta dokar, don jama’a su samu damar fita ko sa samu abin sakawa a baki alfarmar wannan wata na Ramadan.
Kowa da kiwon da ya karbe shi
Sai dai kuma ba a taru an zama daya ba.
Hajiya Chilla Baba Kura Grema cewa ta yi hakika tana goyon bayan wannan kulle, “domin an yi hakan ne don kare lafiyarmu, kuma hakan da aka yi din idan an tabbatar babu cutar hakan zai sa hankalin mutane ya kwanta.
“Kuma ina ganin lokaci ne da gwamnati za ta iya tallafa wa al’umma domin kowa na gida a zaune, duk da dai an fara azumi babu dadi, amma dai jama’a su yi hakuri, komai zai koma daidai”.
Shi ma Modu Aisami, wani mai sayar da kananzir, ya ce yana goyon baya wannan kulle, amma “jama’a na cikin wahala idan da hali kamata ya yi gwamnati ta kawo tallafi.
“Shi wannan kulle ai an yi shi ne domin amfanin mu, mu jama’a, kuma ba a yi hakan don cutarwa ba, don haka ba wai ina da wani abinci da na tara a gida ba ne, illa dan abin da ba za a rasa ba, amma dai kullen zai kasance alheri ne garemu kuma jama’a su yi hakuri a zauna a gida, kwana 14 kamar yau ne, in Allah Ya yarda.
Martanin hukumomi
Aminiya ta yi kokarin samun mataimaki na mussaman ga Gwamna Babagana Zulum a kan harkokin addini, Sheikh Modu Mustapha, amma hakan ya ci tura domin duk lambobin wayarsa suna kashe.
Sai dai wata majiya ta ce gwamnati za ta fara rabon kayan azumi, amma ba ga jama’ar gari ba.
Abin jira a gani dai shi ne ko za a yi rabon, kuma wa za a baiwa?
Hana yaduwar coronavirus
Gwamnatin jihar ta Borno dai ta bi sahun wasu jihohin ne wajen kafa dokar hana fita da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
Mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar ya riga mu gidan gaskiya, sannan alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na nuna cewa zuwa karfe 11.30 na daren 23 ga watan Afrilu, akwai 12 a jihar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.
Tuni dai gwamnonin Najeriya suka bayar da sanarwa cewa sun yi ittifaki a kan su rufe daukacin jihohin kasar har tsawon makwanni biyu.