✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumin bana: Ga zafin gari ga na aljihu

Wata mata da aka bar marayun ‘ya’ya 4 a tare da ita, ta fashe da kuka a lokacin da ta karbi rabonta.

A ranar Litinin da ta gabata ce Musulmin Nijeriya da wasu kasasen duniya suka fara azumin watan Ramadan na bana.

Sai dai azumin na bana ya zo a daidai lokacin da ake tsananin zafin rana, ga kuma tsadar rayuwa da rashin wutar lantarki da sauran abubuwa marasa dadi ga Musulmin Nijeriya.

Aminiya ta gano cewa dole wasu ma’aikata, musamman leburori da sauran mutane suka nemo wasu hanyoyi don rage wahalar azumin.

An kwashe watanni farashin kayan abinci da na kayan masarufi suna tashin gwaron zabo da kaso 80 ko 90 domin wasu kayayyakin farashinsu ninkawa ya yi yayin da wasu farashinsu ya ninka da wani kaso mai yawa.

Kayan abinci irin su shinkafa da wake da sukari tuni suka fi karfin mai karamin karfi inda wasu mutane suka koma cin shinkafar ‘A Fafata’ a Kano ko kuma yin amfani da mazarkwaila a maimakon sukari a sassan kasar nan.

Tun kafin zuwan azumi mutane suke ta fatan cewa kada yanayin tsadar ya kai lokacin azumin duba da cewa lokacin ne ake bukatar abinci mai dan dadi.

Kamar yadda aka saba shekarun da suka gabata ko a gidajen talakawa za ka ga cewa idan aka tashi buda-baki akan soya doya da kwai a hada da dan ruwan lemon ko zobo.

Idan an zo abinci kuma akan dafa shinkafa ko taliya. Sai dai za a iya cewa a wannan lokaci ire-iren wadannan abinci sun fi karfin talaka.

Masu kumbar susa ma sai sun hada da dauriya suke iya cin irin wadannan abincin da aka ambata.

Ana ganin halin da ake ciki na kunci da talauncin yana shafar ibadar mutane kai-tsaye duba da cewa sai mutum yana da natsuwa sannan yake da karfi da karsashin yin ibada.

Yawancin mutanen Jihar Kano da Aminiya ta tattauna da su sun ce suna yin azumi ne a cikin tsanani biyu; tsananin zafin aljihu da tsananin zafin rana.

Malam Isa Adam ya ce ba ya bambance lokacin azumin da na baya. “Ni fa ina ganin babu wani bambamci tsakanin lokacin azumin da lokacin da ba na azumi ba.

“Idan kin lura tun kafin wannan lokaci mutane suke yin azumi (na dole) yanzu sake jaddadawa kawai suke yi,” in ji shi.

Malam Kabiru Mai-mai ya shaida wa Aminiya cewa a wannan azumin bai iya sayen dukkan abubuwan da ya saba saye.

Ya ce, “A da idan azumi ya zo nakan sayi kayan shayi da su kwai da dankali da doya in kai gida.

“Amma a wannan azumin sukari kawai na daure na saya don shan kunu don na ce ko lemon zobo da aka saba yi ba za a yi ba a bana.”

Shi ma wani magidanci mai suna Abdulhamid Ahmad ya ce saboda tsadar rayuwa da ake ciki mutane ba su yi dokin zuwan azumi kamar yadda aka saba yi a baya ba.

“Kin ga a da idan aka ce azumi ya kusanto mutane sun rika dokin su ga azumin tare da yin shiryeshiryen tarar azumin.

“Wadanda suka hada da sayen kayan abincin da ba a a ci koyaushe domin a kyautata wa kai.

“Amma a wannan lokaci babu wani dokin da mutane suka yi na zuwan azumin saboda sun san babu wani abu da za su samu na muwalatin azumi,” in ji shi.

Malam Ali Sanusi ya ce sakamakon tsadar rayuwa da ake ciki ko dabinon da ake fara yin buda-baki ya cire shi daga jerin kayan buda-baki.

“A shekarun baya idan azumi ya zo nakan sayi kwano guda na dabino saboda buda-baki amma a bana na soke sayensa.

“Idan aka sha ruwa sai dai a fara buda-baki da ruwa kawai,” in ji shi.

Wata uwa mai suna Umma Abubakar ta ce, “Kin san azumi abu ne da ake so idan an sha ruwa a dan dafa wani abu mai dadi wanda za a fara ci, idan kafin daga baya a ci abinci sosai.

“ Amma saboda yanayin da aka samu kai, abinci muke ci idan an sha ruwan. Sai dai kasancewar ba haka muka saba ba, abin ya zame wa yarana wani sabon abu wanda sun kasa sabawa da shi.

“A yanzu ba su iya cin abinci sosai. Wallahi ba karamin tausaya musu nake yi ba.”

Ita ma Fatima Ado ta ce yanayin da ake ciki ya hana ’ya’yanta yin azumi, “Saboda a yanzu ba za a iya samun wannan kayan dadin da mutane suka saba ci ba, shi ya sa na hana yarana yin azumi.

“Kin ga idan sun sha ruwa ba za su rika damuna sai na yi musu abin dadi ba. Sai su ci duk abin da ya sauwaka,” in ji ta.

Wani magidanci mai suna Auwal Ibrahim ya ce saboda halin da ake ciki na talauci ba ya iya zuwa yin Sallar Asham.

“Kin san idan mutum.ya ci abincin buda-baki ya tafi masallaci Sallar Asham to cikinsa zazzagewa yake yi.

“Idan ya dawo zai bukaci karin wani abincin, to a halin da ake ciki ina mutum yake da abincin da zai yi ta irin wannan cin.

“Abinci ne idan aka daga shi za a ci da buda- baki da kuma lokacin sahur.”

Da yake bayani, Babban Limamin Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Sheikh Abubakar Muhammad Shitu Samaruddani kan halin da al’umma suka samu kansu, ya ce bayar da zakka kamar yadda Allah Ya umarta na da matukar fa’ida saboda duk wanda ya fitar da zakka ya sauke wani nauyi da Ubangiji Ya yi umurni a kai ga dukkan masu dukiya.

Limamin ya jawo hankalin al’umma kan illar boye abinci da tauye mudu da kuma cin muguwar riba, ya ce wanda duk mai aikata wadannan zai gamu da fushin Ubangiji.

“Tun kafin Ramadan magidanta da dama ciyar da gidajensu da kyar suke yi saboda talauci a wannan lokaci.

“Bisa wannan yanayi da al’umma ke ciki a yanzu, rashin kudi da abin da zai tallafa wa rayuwarsu shi ne babban abin da ke damunsu.

“Za mu iya cewa wadannan abubuwa da muka bayyana a baya suna raunata al’umma wajen tunanin yadda za su tafiyar da rayuwa cikin walwala su da iyalansu,” in ji shi.

A Jihar Yobe, Aminiya ta samu ganawa da wani magidanci da ya ce, “A bana sai dai mu ce “Inna lillahi wa inna ilaihin raji’un!”

Domin kamar yadda Hausawa ke cewa ne daminar bana ba irin ta bara ba, domin a bana abin da za mu ciyar da iyali ma ya zama wani abu daban ballantana sayen kayan abinci na musamman don azumi.”

A cewarsa a halin da ake ciki a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da albashin sa bai wuce Naira dubu 50 ba, kudin ko kwana 10 ba sa isarsa ballantana sayayyar azumi.

Shi ma Malam Muhammadu Isa wani magidanci da ke leburanci cewa ya yi batun tanadin kayan abincin azumi ma bai taso ba, domin a cewarsa abinci yau da kullum ma yaya aka kare ballantana wani abinci daban.

Malam Shitu Mai-shago wani dan kasuwa a Sabuwar Kasuwar Damaturu ya shaida wa Aminiya cewa, a bana sai dai su ce Allah Ya kyauta domin a baya gab da fara azumi da kuma farkon fara azumin sukan yi ciniki sosai, amma a bana kamar ba azumi aka fara ba.

A birnin Ibadan Hedikwatar Jihar Oyo, al’ummar Musulmi masu hali sun ci gaba da taimaka wa ‘yan uwa marasa galihu da kayan abincin buda baki da suka saba yi cikin watan Azumin Ramadan na kowace shekara.

A binciken da Aminiya ta gudanar a Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a Ibadan, ya nuna cewa masu hali daga cikin Hausawan sun aika da nau’in kayan abinci iri-iri zuwa gidajen marasa galihu musamman a cikin kwana 3 na farkon Ramadan.

Sai dai binciken ya nuna cewa an samu ragowar yawan masu hannu da shuni da suka saba taimakon ‘yan uwa Musulmi da kayan abincin a baya.

Kuma an samu karuwar marasa galihu da suka samu kansu cikin tsadar rayuwa a bana.

Har ila yau an samu karuwar irin wadannan Musulmi marasa galihu maza da mata da suke shiga cikin Masallatai a lokutan salloli biyar na kowace rana suna rokon jama’a su taimaka masu da abincin sahur da buda baki.

A baya kafin isowar watan Ramadan, Limamai a wasu Masallatai sun dakatar da irin wadannan mutane yin roko a Masallatansu.

Wani matashin da Allah Ya hore masa abun hannu da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Aminiya cewa “mun kiyasta gidaje guda 250 da muka aika masu da nau’in kayan abinci na shinkafa da wake da taliya da man gyada da madara har da nama ko kifi.”

Wata matar aure da mijinta ya rasu ya bar marayun ‘ya’ya 4 a tare da ita, ta fashe da kuka a lokacin da ta karbi rabonta.

Ta ce “hawayen da ka ga yana fitowa daga idanu na farin ciki nake yi idan na tuna tsawon lokacin da muka Yi rabon mu da cin irin wannan kayan abinci har da nama a ciki”