Almajirai sun ce samun abincin bude bake da sahur na gagararsu a azumin bana, duk kuwa da yawaitar wuraren da ake bayar da abinci sadaka.
Aminiya ta yi duba game da halin da almajiran suke ciki a yanzu da ake yin azumin watan Ramadan.
- Hattara dai mata: Mu yi wa kanmu fada kafin ranar da-na-sani
- Sarkin Musulmi bai halarci jana’izar diyar Sardauna ba
- Tallafin COVID-19: Majalisa ta kalubalanci Minista kan yadda ta kashe N32.4bn
- Yadda Boko Haram ta raba kyautar kudade a Geidam
Kodayake binciken Aminiya ya nuna cewa hakan na faruwa ne sakamakon yawan da almajiran suka yi a gari kamar yadda wani almajiri ya shaida mata.
“Idan kin kula kafin a fara azumi an kawo almajirai da yawa garin nan, hakan shi ya janyo ba kowa ne a cikinmu yake samun abinci a lokacin buda baki ba, duk kuwa da yake akwai wuraren da ake rarraba abincin sadaka,” inji shi.
Yawancin almajiran da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa da farko-farkon lokacin azumi sun rika samun abinci idan suka je bara, amma yanzu abin sai a hankali.
“Amma yanzu gaskiya ba a samu sai dai irin wadanda ke da iyayen gida inda suke yin aikatau su ne kadai ke samun abinci.”
Almajirci da bara
Almajirci kamar yadda aka sani shi ne yadda ake kai yara wasu garuruwa domin neman ilimin Alkur’ani a makarantun allo.
Idan wadanann almajirai suka zo almajircin su da kansu ke neman abin da za su ci ta hanyar yin bara a gidajen mutanen gari ko kasuwanni da sauransu.
Yakan zamanto wani lokaci su samu wani kuma lokacin su rasa. Irin wannan kuwa tana faruwa har a lokacin azumi.
Sai kuma nakasassu da su ma sukan fita domin bara, su nemo abinci.
‘Masu aikatau a gidaje suna samun abinci’
Rabi’u Amadu, almajiri ne a Kano, ya ce, “Kasancewar ina yin aikatau a wani gidan masu hali to ni gaskiya abinci ba ya zama min matsala.
“Idan aka yi buda baki zan karbi abnci a gidan idan zan tafi kuma nakan samui wanda zan yi sahur da shi wanda ma har sai na ba wa wasu daga cikin abokaina.”
Shi ma wani almajiri, Abdurraheem, ya bayyana cewa a yanzu yana samun abinci daga irin wuraren da ake fito da abinci da niyyar ciyarwa.
“Kin san lokacin azumi ana yin abincin ciyarwa a wurare daban-daban don haka nake fitowa irin wannan wuri don samun abin da zan yi buda baki, duk da cewar akan yi kokawa kafin a samu amam dai ina samu.”
Sai dai ba haka abin yake ba ga alamjiri Sahabi Isyaku, wanda ya bayyana cewa gaskiya ba ya samun abinci sai ya yi bara.
“Ni ina yin bara sannan nake samun abincin buda baki, duk da cewar akan dauki lokaci kafin na samu, domin ina tsayawa sai mutane sun dade da fara buda baki sannan sai na yi musu bara.
“Domin idan na yi barar da wuri to ba lallai na samu ba. Kin san ba kowa ne yake da zuciyar tausaya wa almajirai ba.”
‘Yadda muke samun abincin sahur’
Wani almajirin ya bayyana cewa shi da abokansa idan aka yi kiran sallah sukan samu su sha ruwa kawai sannan sai su je su zauna a wani kofar gida don jiran ragowar abincin da za a fito da shi daga gidajen da ke unguwar.
“Mukan zauna mu jira abincin da za a fito da shi don ba wa almajirai daga gidajen da ke wurin.
“A nan za mu samu abin da za mu ci mu sha na buda baki har ma mu samu na sahur.
“Watarana idan kuma ba mu samu da yawa ba sai mu ci na buda bakin mu hakura mu tafi makwancinmu.
“Idan lokacin sahur ya yi sai mu sake fitowa barar abincin da za mu ci.”
‘Akan hana mu abinci a zo ana zubarwa a shara’
Har ila yau almajiran sun koka game da yadda mutanen gari suke kin ba su abinci a lokacin da suke bukata amma sai gari ya waye a rika neman almajirai da za su ci.
Sun kara da cewa sukan je neman abinci a hana su, amma kuma sai da safiya su ga abincin a shara.
“Wani abin damuwa ita ce za ki ga mun yi yawon bara a gidaje don neman abinci ba tare da mun samu ba, amma sai ki ga idan gari ya waye ana ta fito da abinci don bayarwa ga almajirai.
“Duk da yake ana samun almajiran da ke karbar abincin, irin wadanda ba su yin azumi amma ba su da yawa.
“A karshe sai dai ki ga ana zubar da abincin a shara.”
‘Tsadar rayuwa ta sa ba a cika rage abinci ba’
Aminiya ta zanta da wasu magidanta game da yanayin yadda almajirai ke shiga damuwa wajen samun abincin sahur da na buda baki.
Malam Ibrahim Muhammad ya ce, “To kin san dai a yanzu akwai tsadar rayuwa don haka ba kowa ne zai girka abincin da ya fi karfin yawan iyalansa ba.
“A yanzu kowa idanunsa yana kan kayan abincinsa. Su kansu mata suna taka-tsantsan da abinci saboda sun san idan suka yi barna abin da zai biyo baya.”
Shi ma wani magidanci mai suna Ali Sanusi ya bayyana wa Aminiya cewa suna yin iya kokarinsu wajen taimaka wa almajirai da abinci sai dai kawai almajiran ne suke da yawa.
“Gaskiya mutane suna taimaka wa almajirai da abinci, musamaman a lokacin nan na azumi sai dai kawai sun yi yawa don haka ba lallai a gamsar da bukatarsu ba.
“Kin san ana cewa idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai,” inji shi.
‘Azumin bana a cikin kunci muke yi’
Aminiya ta kuma ziyarci sansanin mabaratan a jihohin Legas da Ogun a yankin Alagbado, inda matattara ce ta mabarata guragu.
Daga nan ta ka je dandalin da mabarata mata da yara da dattijai ke taruwa a kan doguwar gadar nan ta Arepo da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a kan iyakar jihohin Legas da Ogun inda suke ke yin dandazo domin yin bara a kan gadar da rana, idan dare ya yi, sai su koma karkashin gadar su kwana mazansu da matansu da yara kanana.
Aminiya ta zanta da mabaratan, wadanda da yawansu suka koka da kuncin rayuwa a lokacin Azumin Ramadan na bana.
Sarkin guragun Alagbado, Malam Abubakar Daudu ya shaida wa Aminiya cewa mabarata na cikin wani hali a lokacin azumi domin taimakon da jama’a ke yi ba ya risker su.
“Yanzu masu badawa ma ta kansu suke, sannan masu hannu da shuni da suke da wadata daman su ba sa bai wa mabarata da nakasassu sadaka, don haka al’amarin sai dai mu gode wa Allah,” inji shi.
Ya ce akwai mutanen da suka ba su shawara su nemi shugaban addinin Musulumci na yankinsu wanda ake kira Baba Addini, domin ya ba su tallafi.
“Sai na ce ba za mu neme shi ba, ai ya san da zamanmu. Ai mai son ya taimake ka ba sai ka nemi ya taimaka maka ba, da kansa zai neme ka ya ba ka taimakon,” inji shi.