✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi na gaskiya 01

Huduba ta FarkoGodiya da hamdala ga Allah.Bayan haka, ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku…

Huduba ta Farko
Godiya da hamdala ga Allah.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yyi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)” (k:3:102).
Ranaku suna shudewa kamar shudewar girgije, shekaru suna wucewa da sauri, alhali mu muna cikin mayen rayuwa muna shagaltatttu. ’Yan kadan ne suke tunani ko tadabburin halin da muke ciki ko makomarmu. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (k:25:62).
Musulmi a cikin shekarunsa abin iyakancewa ne, kuma rayuwarsa gajera ce. Hakika Allah Ya sanya masa wasu ayyukan musamman na laheri, kuma Ya ba shi daga zamani da wuri masu daraja da za su kange shi daga karkacewa su daidaia rayuwarsa. Daga cikin wadannan ayyuka akwai azumin watan Ramadan Mai albarka. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa.” (k:2:183).
A cikin watan Ramadan takun sha’awoyi kan ragu a zukata masu imani. Ayyukan kankan da kai su daukaka a cikin yini da dare. Wani yana rokon afuwa kan gazawarsa, wancan yana rokon dacewa a cikin ayyukan da’arSa, wancan kuma yana isti’aza daga ukubarSa, wani yana fatar kyakkyawar ladarSa, wani kuma ya zikirinSa ya shagaltar da shi daga rokonSa. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya datar da su, yayin da aka haramta wa wasunsu.
Watan Ramadan wata ne na karfi da kyauta, wata ne na raya dare da imani, wata ne na aiki da hakuri. Ba wata ne na rauni da kasala da barci ba. Kasalar wasu masu azumi da komawarsu ga barci a yininsa da karanta ayyuka ya saba wa hikimar yin azumi, bai dace da manufarsa ba.
Musulmin farko sun kasance suna rayuwa ne a cikin Ramadan da zukatansu da hankalinsu, idan dayansu na azumi, hakika shi yana kiyaye yininsa yana mai hakuri kan wahalhalu, yana mai kiyaye dokokin Allah jin tsoronSa. Mai nesa da duk abin da zai bata yininsa ya bata azuminsa. Ba ya furta mummunar magana, kuma ba ya fadin komai sai alheri, in ba haka ba, ya yi shiru. Kuma darensa ya kasance yana kashe shi ne cikin Sallah da tilawar Alkur’ani da zikiri domin koyi da Manzon Allah (SAW).  
Ribar azumi da sakamakonsa falalarsu ba su da iyaka, kidaya ba ta kididdige su, sai dai ba a sanya masu kasala, masu wasa da suke bata watan ga tsunduma cikin barci, ko kai dare a shagunan kasuwanci da kashe dare ana wasa.
Azumi garkuwa ne daga wuta kamar yadda Ahmad ya ruwaito daga Jabir (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Abin sani azumi garkuwa ne da ke kange bawa daga wuta.” Azumi garkuwa ne daga sha’awoyi, domin hakika ya zo a cikin Hadisin Ibinu Mas’ud (RA)  cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Ya ku taron samari! Wanda yake da ikon yin aure daga cikinku, to ya yi aure, domin shi ya fi runtsewa ga ido da kuma kange farji. Wanda kuma ba ya da iko, na hore shi da yin azumi, domin shi garkuwa ne gare shi.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Azumi hanya ce ta zuwa Aljanna, hakika Nisa’i ya ruwaito daga Abu Amama ya ce: “Na zo ga Manzon Allah (SAW) na ce: “Ka umarce ni da wani al’amari da zan rike daga gare ka.” Sai ya ce: “Na hore ka da yin azumi, domin shi babu kamarsa.”   
A cikin Aljanna akwai wata kofa babu mai shiga ta cikinta, sai masu azumi. An karbo daga Sahlu bin Sa’ad (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Lallai a cikin Aljanna akwai wata kofa ana ce da ita: Rayyan. Masu azumi ne za su shiga ta ita a Ranar kiyama, babu mai shiga a cikinta bayansu. Za a rika cewa ina masu azumi? Sai su tashi, babu mai shiga ta cikinta sai su. Idan suka shiga sai a kulle, babu mai shiga a bayansu.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Azumi yana ceton mai yin sa. Hakika Imam Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi bin Amru bin Al-As (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Azumi da Alkur’ani suna ceton bawa a Ranar kiyama. Azumi zai ce: “Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awoyi da rana, Ka ba ni cetonsa. Alkur’ani kuma ya ce: “Na hana shi barci cikin dare, Ka ba ni cetonsa. Ya ce: “Sai su yi ceto su biyun.
Azumi kaffara ce da gafara ga zunubai, domin kyawawan ayyuka suna kankare munana. Hakika (SAW) ya ce a Hadisin Abu Huraira (RA): “Wanda ya yi azumi yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.”
Azumi sababi ne na samun sa’ad a duniya da Lahira. Manzon Allah (SAW) ya fadi a Hadisin Abu  Huraira cewa: “Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi soyuwa a wurin Allah daga kanshin turaren almiski. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buda-baki da kuma in ya hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.  
Shin za mu sanya wa Ramadan wani lokaci ya zama na komawa ga Allah da hisabi ga kai da kyautata inda muka gaza a bangaren Allah?! Shin ko daliban ilimi da masu da’awa za su sanya Ramadan ya zama wani lokaci na jaddada himma da tsarkake niyya? Su ne suke dauke da mafi girman da’awa da cikar gaya. Ko kuwa Ramadan zai kasance wata furs ace da kowane Musulmi zai taimaki dan uwansa azzalumi ko wanda aka zalunta?! Ya taimaki wanda ake zaluna ta hanyar kwato masa abin da aka zalunce shi, ya taimaki azzalumi ta hana shi yin zaluncin, sai muanen kirki su shugabanci al’ummar Musulmi. Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ga mawadata da masu bushasha su warware bukatun fakirai, su yi shukura kan ni’imar da aka yi musu ta hanyar ajiye ta a inda Wanda Ya ba su ni’imar Ya ce, ta yadda za su iya ceto mayunwata daga cikin al’ummar Musulmi? Imaninsu yana iya fadawa ga hadari, idan suka gaza ciyar da mayunwatansu ko tufatar da marasa tufafinsu ko shayar da masu jin kishinsu. Ko kuwa Ramadan zai kasance wani lokaci da kowane Musulmi zai fahimci kasala da rashin kazar-kazar na iya jefa shi ga aikata kaba’ira, ta yadda zai ciru daga giba da annamimanci da mummunan zato da wulakanci da raina dan uwansa Musulmi?
Ramadan ya ku bayin Allah! Babbar makaranta ce da muke samun horo a darensa da ranarsa, gabbanmu su karfafa da shifttarsa har sai dukkansu sun yi kamar yadda Ubangijinta, Mahaliccinta Ya yi nufi. Ya zo a cikin Hadisin kudusi cewa: “BawaNa ba zai guje yana kusantaTa da nafilfili ba, har sai na so shi. Idan kuma Na so shi, sai in kasance jinsa da ake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damka da shi da kafarsa da yake tafiya da ita.” Buhari ya ruwaito.