Tun daga lokacin da watan Azumin Ramadan ya gabato, farashin kayayyaki kama daga kayan abinci da na masarufi da tufafi da kayan marmari suka yi tashin gwaron zabo a kusan dukkan kasuwannin da ke Jihar Kano.
Binciken da Aminiya ta gudanar a wasu kasuwannin Kano ya nuna cewa duk da tashin farashin kayayyakin, jama’a na ci gaba da tururuwa zuwa kasuwannin don sayen kayayyakin bukatun yau da kullum.
Ziyarar da Aminiya ta kai Kasuwar Singa wacce ke hada-hadar kayan abinci a jihar, ta iske farashin shinkafa ’yar waje ya tashi daga farashinsa na asali na Naira dubu 14, inda a yanzu ya koma tsakanin Naira dubu 16 zuwa dubu 17. Haka taliya da makaroni wadanda a da ake sayar da katan dinsu a kan Naira 3,100 yanzu kuma ya koma Naira 3,300.
Haka lamarin yake idan aka koma kan sukari da man girki da sauran kayayyakin abincin da suka shafi kayan shayi da kwai da naman kaji da sauransu.
Aminiya ta kai ziyara Kasuwar Kantin Kwari wacce ake hada-hadar kayayyakin tufafi inda ta gano tuni kayayyakin da suka kama daga kan atamfa da leshi da shadda da sauran yadudduka, yawanci farashinsu ya daga daga yadda aka san su tun farko.
Alhaji Umar Indabawa ya shaida wa Aminiya cewa duk da cewa akwai wasu kayayyakin da suka samu dan kari amma ba kamar shekarun baya da ake yin kari mai yawa ba.
“A gaskiya bana kayayyakin tufafi ba su yi tashin gwaron zabo kamar na sauran shekarun baya ba. Idan ma an samu kari to kadan ne da bai taka kara ya karya ba, domin kusan dukkan kayan da muke sayarwa dama can haka farashinsu yake. A yanzu haka ana sayar da atamfa karamar a kan Naira dubu biyu wacce a baya kudinta Naira 1,600 zuwa Naira 1,700 ne,” inji shi.
Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Bulawus ta Kano, Alhaji Dayyabu Salisu Sani ya bayyana cewa duk da cewa a yanzu farashin kayansu bai tashi ba, amma sun san akwai yiyuwar samun wannan barazana yayin da kawanakin Sallah suka gabato.
A cewarsa yawancin abin da ke janyo tashin farashin kayayyakinsu shi ne yin amfani da jirgi wajen shigo da kayan a duk lokacin da suka yanke a kasuwa. “Za ki samu wani lokacin saboda bukatar kayan da ake yi a kasuwa sai an tafi an sayo kayan a kasar waje, kuma ko a gida ne kasancewar idan aka sayo kaya akan dauki lokaci ba su zo ba, don mu samu biyan bukata cikin sauri sai mu yi amfani da jirgin sama. To idon muka yi haka a harkar ya zama dole mu kara wa kayayyakin namu kudi don mu ga mun fitar da kudin da muka kara wajen saro kayan,” inji shi.
Yawancin masu sayen kayayyakin da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana bacin ransu game da yadda ake samun tashin gwaron zabo a duk lokacin da azumi ko Sallah suka gabato, duk kuwa da kiraye-kirayen da malamai ke yi a kan hakan.
Malam Iro Musa ya bayyana cewa lokacin da ya je kasuwa ya samu farashin kayayyaki sun tashi ransa ya baci kwarai da gaske sai dai hakan bai hana shi yin sayayyarsa ba. A cewarsa, bukata ce ta fito da shi. Ya ce, “Dole mutum idan ya samu haka ransa ya baci, sai dai ba yadda mutum zai yi domin yana bukatar kayan. Babban abin da ke bata min rai shi ne ’yan kasuwarmu ba su lura da abin da abokan zamanmu da ke kasar nan ke yi a duk lokacin da bukukuwansu suka taso, inda sukan rage farashin kayayyaki, to me ya sa mu Musulmi ba za mu yi hakan ba?”
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce yawanci abubuwa uku ne suke sanya ’yan kasuwa kara farashin kayayyaki, wadanda kuma idan gwamnati ba ta sa hannunta a ciki ba, abubuwan ba za su taba gyaruwa ba.
“Wannan ya zama wata al’ada ce ta dan kasuwa, idan suka ga ana garajen sayen abu to za ki ga an kara masa kudi. Haka kuma kananan ’yan kasuwa suna daukar irin wannan lokaci a matsayin lokacin mayar da asarar da suka yi a baya. Misali mai sayar da tumatir da dankali da ya sha yin asara a baya, don haka lokaci ya yi da zai mayar da asararsa,” inji shi.
Malamin ya yi kira ga gwamnati da manyan masu kudi su sa hannunsu a cikin irin wannan lamarin don a samu sauki a cikin lamuran. “Ina kira ga gwamnati da masu kudinmu su sa hannu a cikin harkar farashi, ba wai lallai su kayyade farashi ba, amma su yi wani abu na rage farashin kayayyaki yadda kananan ’yan kasuwa za su samu da sauki.
“Kuma su tilasta ragin a kan dillalansu har ya gangaro kan talaka. Za ki ga a kasashen duniya ana yin kamar wani abu na gwanjo inda ake ware wani lokaci na musamman na bukukuwa a zabge farashin kayayyaki. Misali, idan ana sayar da abu Naira 10 sai a mayar da shi Naira 4,” inji shi.
A Jihar Bauchi ma labarin bai canja ba, domin kuwa farashin wasu daga cikin kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabo a kasuwanni, yayin da wasu kuma aka samu sauki a kansu fiye da yadda aka saya a shekarun baya.
Wakilin Aminiya da ya zaga wasu daga cikin kasuwannin, ya ce farashin dankalin Turawa da doya sun haura sama. Ya ce Kafin azumi, karamin buhun dankalin Turawa ana sayar da shi ne a kan Naira dubu 6 amma bayan da aka shiga azumin sai ya koma Naira dubu 9, yayin da babban buhu ake samunsa a kan Naira dubu 18 zuwa dubu 20.
Ya ce farashin kayan gwari kuwa yana tsaka-tsaki saboda karancin kayan da ake fama da shi a yanzu. Yayin da farashin kayan marmari kuma kamar lemo da kankana da gwanda aka samu sauki, sakamakon matakan da kungiyar masu sayar da kayayyakin marmari ta kasa ta ce ta dauka.
Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Kayan Gwari ta Jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya ce a bana azumi ya zo a lokacin zafi, lokacin da ba kasafai ake samun kayayyakin gwari kamar tumatir da attarugu da tattasai ba, amma albasa tana da sauki sosai.
Ya ce a da suna samunsu a dukkan kananan hukumomi 20 da ke Jihar Bauchi, amma a yanzu ana samun wasu ne a yankin Kirfi, kuma ana sayowa daga Katsina har zuwa kasar Nijar.
Ya ce yanzu a tudu ake noman su kuma kyansu bai kai na lokacin sanyi ba. “Ana samun kwando n tumatir daga Naira dubu biyu zuwa dubu uku, a baya yakan kai har Naira dubu biyar zuwa shida. Yayin da karamin buhu (solo) ake samunsa a kan Naira dubu takwas na tattasai da attarugu saboda yanzu ana zuwa nema daga Kudancin kasar nan; musamman Jihar Legas amma farashin da sauki.
Malam Auwal Suleiman shi ne Sakataren Kungiyar Masu Sayar da Kayan Marmari ta Jihar Bauchi, ya ce buhun lemon zaki mai bawo yanzu suna sayar da shi ne a kan Naira dubu hudu zuwa dubu biyar. Kuma ana sayar da kwallon kankana babba a kan Naira 300, mai bi mata Naira 200 da kuma na Naira 100.
Sakataren Shiyya na Masu Kayan Gwari na Najeriya, Alhaji Mahmud Abdullahi Ahmad ya ce “Uwar kungiyarmu ta kasa ce ta dauki kudi ta shirya da mutanen Jihar Binuwai da Jihar Ondo, kan su sayar mana da lemo kada a kara farashi. Shi ya sa aka samu sauki amma a bara ya kai har Naira dubu tara a buhu.”
Wadansu magidanta, Hajiya Addaji Muhammad da Alhaji Suleiman Aliyu sun ce farashin wake bai tashi ba, domin suna sayen kwano daga Naira 200 zuwa 240, kuma suna sayen shinkafa ’yar Najeriya kwano a kan Naira 430 zuwa 450, ’yar kasar waje kuma suna sayen kwano a kan Naira 470 zuwa 500. Sun ce farashin bai tashi ba, duk da shigowar azumi
Magidantan sun ce doya da dankalin Turawa sun yi tsada, domin kwaryar doya a da ana samun ta a kan Naira dubu 20 zuwa dubu 30 yanzu kuwa daga Naira dubu 35 ne zuwa dubu 50 ake sayar da kwaryar doya.
Sun roki gwamnati ta taimaka wajen samar da kayayyakin domin jama’a su samu sauki.