✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi da hukunce-huluncensa

Limamin Masallacin Izala Mary Slessor, Kalaba Ganin cewa nan da kasa da mako biyu za mu fara azumin watan Ramadan, daga yannzu zuwa lokacin da…

Limamin Masallacin Izala Mary Slessor, Kalaba

Ganin cewa nan da kasa da mako biyu za mu fara azumin watan Ramadan, daga yannzu zuwa lokacin da Allah Ya so za mu karkata wajen gabatar da hudubobin da suka shafi azumi da hukunce-hukuncen da suke rataye da shi da sauran abu buwan da suka shafe shi:

Huduba ta farko
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya farlanta azumi a kan bayinSa muminai a wata mai girma. Ya sanya daren lailatun kadari ya fi watanni dubu alheri. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, mulki da godiya naSa ne, kuma Shi ke da halitta da juya al’amura, Shi ke da izza da buwaya. Ina shaidawa shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu binsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, yaku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah a kan hakkin jin tsoroSa, kada ku yarda ku mutu face kuna Musulmi. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa. Kwanuka ne kidayayyu, wanda ya kasance marar lafiya ko a kan tafiya, to ya rama a wasu kwanuka na daban.”
Ya ku Musulmi! Azumi domin Allah ibada ce mai girma, babu wani koma bayan Allah da zai iya bayyana gwargwadon ladanta. Azumin watan Ramadan daya ne daga cikin rukunan Musulunci biyar da Allah Ya shar’anta ga bayinSa a matsayin rahama da kyautatawa da kariya da garkuwa daga wuta.
Allah Ya farlanta azumin watan Ramadan a kan muminai, Ya lizimta musu yin sa ta hanyar da zai gadar da takawa a zukatansu, ya rusa ganuwar sha’awa daga zukatansu. Sai su riski fa’idojin azumi a jiki da ruhi da lafiya da zamantakewarsu. Don haka ne a karshen ayar Allah Madaukaki Ya ce: “tsammaninku za ku yi takawa.” Kuma daga cikin rahama da ludufin Allah a kan Musulmi, sai Ya aiko musu da azumin tare da wasu abubuwa daga cikinsu akwai cewa: Shi Allah Ya ba su labarin cewa azumin da aka faralta musu ba shi ne karo na farko ba a tarihin addinai. Ya ce, “Kamar yadda aka wajabta a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa.” Idan mutum ya san an kallafa masa wani abu ne da aka kallafa wa na gabaninsa, sai ya ji saukin aikata shi, ya sami karfin guiwa a kansa, har ma ya yi kokari wajen yin sa ciki inganci. Sannan Madaukaki Ya ce, “’yan kwanaki ne kidayayyu,” wadanda yanzu za su zo su wuce. Haka ne, yanzu azumi zai zo, yanzu zai wuce. Azumi bai zama ba, face ana yin a wuni kuma wata daya kacal a shekara, saura a huta a ci halal mai dadi a cikinsu. To me mutum zai ragu da shi? Wannan rahama ce da kyauta daga Allah Mai girma da jin kai daga Mai rahama.
Daga ciki akwai kuma cewa, “Allah Ya yi sauki ga tsoho da tsohuwa da ba za su iya azumin ba, cewa su ciyar da miskini a kowace rana, idan za su iya yin hakan, saboda fadin Ibin Abbas (RA) game da fadin Madaukaki: “A kan wadanda suke yin sa (azumi) da wahala akwai ciyar da miskinai.”
Wannan ma’ana ya hada da marar lafiya da bai sa ran warkewar ciwonsa. Haka mai ciki da mai shayarwa da take jin tsoron halaka ko tagayyara, sai ta sha ta rama daga baya.
Daga ciki har wa yau Allah Ya sanya azumin watan wata alama na haduwar al’umma a duniya don yin ibadoji da zikiri da tilawar Alkur’ani da tafsiri da tsentesni da gafarta wa juna da ninkuwar ayyuka. daukacin Musulmi a duniya masu bambancin jinsi ko launi, fakirai da mawadata, malamai da jahilai, a kowane gari da birni da kauye da unguwa da lungu, suna yin wadannan ibadoji a lokaci guda, babu bambancin ra’ayi ko zabi, a’a kowa yana azumtar wata guda ne, watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.
Daga ciki akwai cewa Allah Ya halatta wa Musulmi bayan faduwar rana su sadu da matansu, su ci abinci, su sha abin sha, ya alla mutum ya yi barci ko bai yi ba, domin a farkon faralta azumi an haramta musu ci da sha da jima’i bayan sun yi barci. Sai wadansu suka koka kan haka sai aka saukaka musu, aka halatta musu dukkan wadannan abubuwa a cikin dararen azumi. Sai Allah Ya ce “An halatta muku a daren azumi ku sadu da matanku, su tufafi ne a gare ku, ku ma tufafi ne a gare su. Allah Ya san kuna ha’intar kawunaku, amma Ya gafarta muku, kuma Ya yafe muku, yanzu ku rungume su, ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku game da su, ku ci, ku sha har farin zaren alfijir ya bayyana daga baki, sannan ku cika azumi zuwa dare.” Dukkan wannan da waninsa sauki ne Allah Ya yi a kan muminai. Don haka madalla da su kan azumin watansu, madalla da su kan saukin da suka samu daga Ubangijinsu. Allah Madaukaki Ya ce: “Allah Yana nufin sauki ne a gare ku, ba Ya nufin tsanani a kanku, domin ku cika kidayar, kuma ku girmama Allah a bisa abin da Ya shiryar da ku, tsammaninku za ku gode.”
Azumi shi ne kamewa daga ci da sha da jima’i da makamantansu, da niyyar neman yardar Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana. Cikarsa da kamalarsa shi ne a guji aikata laifuffuka da kauce wa fadawa a cikin haram. Saboda fadinsa (SAW) “Duk wanda bai bar maganar zur ko aiki da ita ba, Allah ba Ya bukatar ya bar abincinsa da abin shansa.”
An farlanta azumi ne a shekara ta biyu bayan hijira, kuma Annabi (SAW) ya yi azumin Ramadan na shekara tara.
Azumi yana wajaba da daya daga cikin abubuwa biyu, ko dai da ganin jinjirin wata, daga mutum iyu adalai ko taron jama’a, ko kuma da cikar Sha’aban kwana 30. Saboda fadinSa Madaukaki: “Wanda ya halarci watan daga cikinku ya azumce shi.” Da kuma fadinsa (SAW), “Idan an boye muku (jinjirin watan Ramadan), to ku cikata watan Sha’aban kwana 30.”
Ba a lura da masaukan wata ko girman jinjirin wata da kankantarsa a yayin kamawar watan. Domin ba a samu cewa Manzon Allah (SAW) ya yi hukunci da masaukan wata ko girmansa ba, ko dogaro da hakan wajen tabbatar da wajibcin azumi ko idi ba. Amma ya inganta daga gare shi a aikace da umurni cewa: “Ku yi azumi domin ganinsa (jinjirin wata) kuma ku sha ruwa (Sallar Idi) don ganinsa. Idan aka boye muku shi, ku cika kidayar Sha’aban talatin.”
Ya wajaba a kan bawa ya marabci wannan wata mai girma da hamdala da shukura da yabo ga Allah da karbarsa da farin ciki da jin dadi. Sannan ya himmantu ga bayar da hakkokin azumi, ya raya wuninsa da azumi da tilawar Alkur’ani, ya raya darensa da tsayuwar dare da addu’a da kankan da kai ga Allah.
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana albishir ga sahabbansa da gabatowar azumin Ramadan. Yana cewa: “Hakika watan Ramadan ya zo muku, watan albarka, da Allah Ya wajabta azumtarsa a kanku, a cikinsa ana bude kofofin Aljanna a rufe kofofin wuta a daure shaidanu, a cikinsa akwai daren da ya fi watanni dubu alheri. Wanda aka haramta masa alherinsa hakika an hana shi babban rabo.” Muna rokon Allah kada Ya haramta mana wannan alheri, kuma muna fata falalar wannan dare mai albarka. Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah Mai girma gare ni da ku daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa lallai Shi Mai yawan gafara ne Mai jinkai.