✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi da hukunce-hukuncensa (3)

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa ribi-ribi

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma farilla ne da Allah ya wajabta a kan bayinsa.

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa ribi-ribi. Allah Madaukakin Sarki ya raba azumi zuwa gare Shi, saboda girmama shi da daukaka shi.

Wasu daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi azumi:

  • Zakkar Fidda-Kai:

Ana fitar da Zakkar Fid-da-Kai ne a lokacin da azumi ya zo karshe. Kuma ta wajaba a kan dukan Musulmi, yaro da tsoho, namiji da mace, da da bawa. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne wanda ya tsarkaka (da imani) ya samu babban rabo. Kuma ya ambaci sunan Ubangijinsa, sa’an nan ya yi Sallah.” (K:87:14-15).

Abu Dawud da Ibn Majah da Darul Kudni sun ruwaito Ibn Abbas (RA) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi umarni a fitar da Zakkar Fid-da-Kai ga kowane Musulmi. Zakkar Fid-da-Kai tana tsarkake azumin mutum daga dukan dauda da abubuwan da suke iya nakasa shi. Ana bayar da ita ga matalauta Musulmi.” Duk wanda ya fitar da ita kafin Sallar Idi shi ya yi ti bisa shari’a. Wanda ya fitar da ita bayan sa sauko daga Idi, to tana daya daga cikin sadakoki ne kawai. Yayin da ake fitar da zakkar ana fitar da Mudun Nabiyyi hudu ko sa’i daya ga kowane mutum daya na abincin da mutanen wurin ke ci, kamar shinkafa da masara da dawa da gero da dabino da alkama da sauran nau’in abincin da ake iya ajiyewa.

Dole ne magidanci ya fitar wa kansa da matarsa ko matansa da ’ya’yansa da barorinsa da duk wanda ke karkashin kularsa.

Bayar da Zakkar Fid-da-Kai, kamar bayar da zakka take, ana bayar da ita ga nau’o’in mutum takwas da shari’a ta tanada. Don haka ya kamata a bayar da Zakkar Fid-da-Kai domin matalauta Musulmi su gudanar da bikin Sallar Idi cikin annashuwa da farin ciki.

  • Sallolin Idi:

Sallolin Idi su ne bukukuwan Musulunci guda biyu a shekara, wato:

  1. Karamar Sallah (Sallar Idil Fidiri) da ake yi bayan kammala azumin watan Ramadan.
  2. Babbar Sallah (Sallar Layya) da ake yi bayan kammala aikin Hajji.

Wadannan su ne bukukuwa biyu da suka zo a bisa koyarwar Manzon Allah (SAW). Wadannan idoji biyu sun wajaba ga wanda zai iya zuwa Sallar Juma’a. Har Manzon Allah (SAW) ya yi wafati bai bar daya daga cikin idojin nan biyu ba. Kuma ya yi kira ga mutane su rika halartarsu, don haka ya kamata Musulmi su rika alfahari da wadannan bukukuwa biyu na Idi, kuma su yi su cikin natsuwa kada wajen nuna farin ciki su aikata sabo ko barna. Su sani bukukuwa ne da Allah da ManzonSa (SAW) suka yi umarni a yi. Kuma su fahimci cewa duk wani biki da ba Allah da ManzonSa (SAW) suka ce a yi ba, bai da daraja.

Ya kamata malaman addini su rika gabatar da wa’azi da nasihohi a kan yadda jama’a za su gudanar da bukukuwan ba tare da cusa wasu bidi’o’i ba.

  • Mata da Sallar Idi:

Matan aure suna iya halartar Sallar Idi, haka ’yan mata da kananan yara ya halatta su je masallacin Idi, matukar za su kiyaye shari’a a yayin fitar. Amma matar da ke zaman takaba saboda rasuwar mijinta ba za ta halarci masallacin Idi ba.

Uwar Muminai Asiya (RA) ta ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu umarnin zuwa Sallar Idi, kuma a cikinmu akwai yara mata da suka yi kusan balaga da wadanda suke jinin haila. Sai ya ce, wadanda suke jinin ba za su yi Sallah ba, sai su koma gefe kawai. Sai wata mace ta ce, ba ta da tufafi, sai ya amsa mata cewa: “A cikinku wata ta ba ta tufafin da za ta sanya.” Buhari da Muslim suka ruwaito. A wata ruwayar ta Muslim kuma: “Wadanda suke jini, sai su tsaya a bayan masu Sallah, amma su rika kabbarorin tare da masu Sallar.” Fitar mata zuwa Sallar Idi ibada ce, sai dai idan magidanci ya tsammaci za a iya samun matsala zai iya hana matarsa zuwa masallacin Idin.

  • Lokacin Sallar Idi:

Za a iya gabatar da Sallar Idi daga lokacin da rana ta fito ta dago sama, wato lokacin da shari’a ta yarda a yi sallar nafila har zuwa lokacin da rana za ta kai tsakiyar sama, ko tsakiyar zafinta.

  • Wurarin da ake Sallar Idi:

Wurin da ya kamata a yi Sallar Idi shi ne sarari kamar hamada ko fako ko filin da ba ginanne ba. Za a iya yin sallar a wani wuri idan hamadar za ta iya yin illa ko wurin yana da cabi ko ruwa ya kwanta. Manzon Allah (SAW) yana gabatar da Sallar Idi a kan yashin hamada. Masallacinsa ya fi hamadar, amma duk da haka yakan bar masallacin ya tafi hamadar. Wannan wata Sunnah ce mai karfi. Matukar babu wata lalura a yi Sallar Idi a wajen gari baya ga wadanda suke Harami a Makka. Malamai sun yi ittifaki cewa Sallar Idi a fili ta fi lada a kan yi a ginannen masallaci. Abu Sa’idul Khudri (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) yakan je filin Baki’a (wani fili a wajen Madina) don ya gudanar da Sallar Idi.” Buhari da Muslmi suka ruwaito. Don haka a Makka ne kawai aka yarda a gabatar da Sallar Idi a cikin masallacin Harami.

  • Kiran Sallah da Ikama:

Yayin gabatar da Sallar Idi ba a yin kiran Sallah ko ikama. Ibn Abbas (RA) ya ce: “Ba a kiran Sallah kafin Sallar Idi.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi. Jabir (RA) ya ce: “Ba a kiran Sallah ko ikama yayin Sallar Idi.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Imam Malik ya ce: “Wannan shi ne koyarwar Manzon Allah (SAW) kuma babu wata jayayya a kai.”

  • Yawan kabbarori yayin Sallar Idi:

Sallar Idi raka’a biyu ce. A raka’ar farko liman da mamu a bayan Liman ya fada za su yi kabbarori bakwai a bayyane. Wadannan kabbarori bakwai ba su hada da kabbarar harama (ta farko ba). Daga nan sai liman ya yi karatun Fatiha da Sura a bayyane. Raka’a ta biyu kuma kabbarori biyar bayan kabbarar tasowa daga raka’ar farko.

Mazhabobi sun yi sabani kan yawan kabbarorin da ake yi lokacin Sallar Idi. Mazhabar Malikiyya da Hambaliyya sun ce kabbarori bakwai da ake yi a raka’ar farko sun hada har da ta harama. Amma Shafi’iyya sun ce bakwai din ba da ta farko. Wannan sabani ba wani abin damuwa ba ne saboda ya ginu ne kan fahimtarsu ga wasu Hadisai. Allah Shi ne Mafi sani.

Allah Ya amshi ibadojin da muka gabatar a cikin wannan wata mai albarka, kuma Ya dawo mana da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu da sauran kasashen Musulmi.

 

Malam Umar ’Yanleman, Cibiyar Al’adun Musulunci a Najeriya (ICCN) Abuja. Za a iya samunsa ta: 08066441995