Shi kuma Salam bin Abu Mudi’u ya ce: “kattada yana sauke Alkur’ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku. Idan goman karshe suka zo, sai ya rika saukewa a kowane dare.” (Siyar A’alamin Nubla’i, 5/276).
Rabi’u bin Sulaiman ya ce: “Imam Shafi’i ya kasance yana sauke Alkur’ani sau sittin a cikin watan Ramadan.” (Siyar A’alamin Nubla’i, 10/36). Akwai misalan haka da dama.
Tsayuwar Ramadan:
An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon (SAW) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (Sallar Tarawihi ko Asham) yana mai imani kuma domin Allah kawai, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Aliyu bin Al-Madani ya ce: “Suwaidu bin Ghafalata ya rika yi mana limanci a tsayuwar Ramadan har ya kai shekara 120 a duniya.” (Siyar A’alamin Nubla’i, 4/72).
Yin azumin Ramadan bisa imani kuma domin Allah kawai da yin nafilfilin dare bisa imani kuma domin Allah kawai da raya daren Lailaul kadari bisa imani kuma domin Allah kawai, suna sa mutum ya samu gafara da ’yantuwa daga wuta. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi wadannan abubuwa uku an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa. Kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito daga Abu Huraira.
Kafin mu karkare dan wannan rubutu, za mu tunatar da kanmu kan wasu hadisai guda biyu: Hadisi na farko shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan watan Ramadan ya zo akan bude kofofin Aljanna a rufe kofofin wuta kuma a daure shaidanu.” Muslim ya ruwaito a Babin Falalar Watan Ramadan, a duba Hadisi na 1079. Alkali Iyal ya ce: “Ana iya daukar bude kofofin Aljanna da abin da Allah zai bude ga bayinSa na su samu damar gudanar da ayyukan da’a a wannan wata, wadanda ba a samunsu a waninsa, kamar yin azumi da tsayuwar dare. Haka kuma kulle kofofin wuta da daure shaidanu na nufin hana mutane damar aikata ayyukan sabo.” (An cirato ne daga Sharhin Muslim na Annawawi, 7/188).
Hadisi na biyu shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya turbude hancin mutumin da aka ambace ni a wurinsa, amma bai yi min salati ba. Allah Ya turbude hancin mutumin da Ramadan ya shigo sannan ya fita amma bai yi abin da za a gafarta masa ba. Kuma Allah Ya turbude hancin mutumin da tsufa ya riski iyayensa suna tare da shi, amma ba su yi sanadin shigarsa Aljanna ba (saboda rashin kyautatawarsa gare su)” (Tirmizi Hadisi na 3545 da Ahmad Hadisi na 7402, kuma Ibnu Khuzaima ya ruwaito makamancinsa, Hadisi na 1888).
’Yan uwa da wannan ya kamata wadannan Hadisai biyu su tayar da tsiminmu wajen ganin mun yi tilawar Alkur’ani da tsayuwar dare da sauran ayyukan alheri a cikin wannan wata mai albarka, domin neman yardar Allah kawai, ba domin riya ko jiyarwa ba.
A karshe muna yi wa ’yan uwa masu yin tahajjud cikin lasifika suna hana sauran mutane yin barci, su yi kokari su guji hakan, domin kada garin neman lada a samu zunubi. Saboda sallar dare ana so ne mutum ya yi ta a boye, a lokacin da sauran mutane suke barci. Idan aka bude lasfika ya zamo an tashi mutane daga barci ke nan, kuma hana mutane barci ko Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba, ya saba wa koyarwar Musulunci. Mutane suna da ’yancin yin barci Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba a cikin dararen watan Ramadan, kada a tashe su saboda ibadar da Musulunci ya fi so a yi ta a boye.
Zakar Fidda Kai:
Zakkar Fidda Kai ko Zakkar Kono kamar yadda wadansu ke fada. Kalmar zakka a lugga tana nufin tsarki da karuwa da yabo da albarka. Wadannan kalmomi duk Alkur’ani ya yi amfani da su. Kalmar Fitr a lugga kuma tana nufin bude wani abu, kuma daga nan ne aka jinigna ta ga mai azumi saboda yana bude bakinsa domin cin abinci.
A shari’a kuma Zakkatul Fitri na nufin zakkar da ake bayarwa bayan kammala azumin Ramadan.
Zakkar Fidda Kai, Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW), Allah Ya farlanta azumi, shi kuma Manzo (SAW) ya farlanta zakka bayan kammala azumin. Bin Manzon Allah (SAW) kuma bin Allah ne, saboda Allah Madaukaki Ya ce: “Abin da Manzon (Allah) ya zo muku da shi, ku rike shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu.” (Hashri:7). Kuma Allah Ya sake cewa: “Wanda ya yi da’a ga Manzon (Allah), hakika ya yi da’a ga Allah.” (Nisa’i: 80).
Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
Shi kuma Salam bin Abu Mudi’u ya ce: “kattada yana sauke Alkur’ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku.…