Akalla ‘yan mata miliyan daya ne za a raba wa audugar mata kyauta domin bikin a ranar jinin al’ada da duniya.
Za a raba musu audugar matan ne domin bikin zagayowar ranar jinin al’ada ta duniya na wannan shekara.
Ministan Harkokin Mata da Walwalar Jama’a Paulen Talen ta ce tallafi da ake rabawa ya kunshi kula da lafiyar ‘yan mata.
Paulin Talen ta ce baya ga tallafin abinci audugar za ta saukaka wa ‘yan matan gudanar da harkokinsu cikin walwala.
- Matar da ta ‘kashe diyarta’ za ta je gwajin kwakwalwa
- Yadda Buhari zai yi bikin cika shekara biyar a mulki – Fadar Shugaban Kasa
- Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati
Ta jaddada bukatar hukumomi da attajirai da iyaye su taimaki ‘yan mata musamman a lokacin jinin al’ada.
Ta haka ne ‘yan matan za su samun audugar mata cikin sauki a lokacin jinin, inji wakiliyarta Funke Oladipo.
Ita ma jawabinsa a wurin taron, Misis Tayo Arinle ta gidauniyar Tabitha Cumi Foundation (TCF) ta koka.
Ta nuna damuwa cewa rabon kayan tallafin da ake yi a kasar nan bai lura da bukatun ‘yanmata a lokacin al’ada ba.
Gangamin ya gudana ne da hadin gwiwar TCF, Mercy Corps da Ma’aikatar Mata ta Tarayya.
An yi shi ne domin wayar da kan ‘yan mata a Durumi Mpape a yankin Birnin Tarayya Abuja.