Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023.
Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun yi nasara,” in ji shashen Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU a shafin X a ranar Laraba.
- Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
- Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
Sanarwar ta ce za a yi maraba da Gabon “ta dawo nan da nan, ta ci gaba da shiga ayyuka” a sakatariyar Tarayyar Afirka.
An dakatar da Gabon a lokacin da Janaral Brice Oligui Nguema ya ƙwace mulki bayan kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo, wanda iyalinsa suka yi mulki tsawon shekaru 55.
Nguema ya yi alkawarin miƙa mulkin ƙasar mai arzikin man fetur ga farar hula bayan shekaru biyu na riƙon ƙwarya, kuma an zaɓe shi a matsayin shugaban farar hula da kashi 94 na kuri’un da aka kaɗa.
Sabon kundin tsarin mulkin da aka samar ya tanadi cewa shugaban ƙasar zai yi mulkin ƙasar da faffaɗan iko.
Matakin da Tarayyar Afirka ta ɗauka ya biyo bayan taron da aka yi a makon da ya gabata tsakanin Nguema da shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, inda Nguema ya nemi goyon baya ta hanyar janye masa takunkuman.
Kasar mai yawan mutane miliyan 2.3 tana fama da rashin ayyukan yi, da katsewar lantarki da rashin ruwan sha, da basussuka a suka yi wa gwamnati katutu duk da arzikin mai da take da shi.