Hukumar Lafiya ta Tarayyar Afirka AU ta sanar da cewa adadin masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a nahiyyar.
AU ta bayyana hakan ne yayin da ta fitar da alƙaluman mutum 18,737 da suka kamu da cutar ƙyandar biri tun daga farkon wannan shekara.
Hukumar ta ce a cikin wannan adadi, har da kimanin mutum 1,200 da suka harbu da cutar a mako guda.
Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa ta Afirka ta ce an samu ɓullar cutar a ƙasashen nahiyyar 12.
Cibiyar ta ce kawo yanzu cutar ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 541, da adadin mace-macen ya kai kashi 2.89 bisa 100.
Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar ƙyandar biri wato mpox a matsayin gagarumar annoba da ke buƙatar ɗaukin gaggawa.
Cutar dai ta fi ƙamari a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango da annobar ta bazu a dukkan lardunan kasar 26.
Rahotanni daga Burundi na cewa an samu ɓullar cutar a mutane 173 da ake ci gaba da gudanar da bincike.
An dai samu rahotannin bullar cutar a karon farko a wajen nahiyar Afirka a ƙasashen Sweden da Pakistan.