✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ATM din Najeriya zai daina aiki a kasashen ketare

  A ranar Litinin da ta gabata ne wasu daga cikin bankunan kasar nan suka ce daga ranar 1 ga watan Janairun badi, duk wanda…

 

A ranar Litinin da ta gabata ne wasu daga cikin bankunan kasar nan suka ce daga ranar 1 ga watan Janairun badi, duk wanda ke da asusun ajiya a wasu bankunan Najeriya, ba zai iya cire kudinsa ba a kasashen waje kamar yadda aka saba.
Bayan daukar wannan mataki jama’a sun ci gaba da mayar da martani a kan matakin.
Wasu daga cikin ’yan kasar nan musamman dalibai a kasashen ketare na ganin cewa matakin zai jefa su cikin tsaka mai wuya.
daya daga cikin bankunan na cewa karancin kudin kasar waje ne ya sa  suka dauki wannan mataki.
A yanzu haka dai darajar Naira na kara faduwa idan aka kwatanta da Dalar Amurka sannan faduwar farashin man fetur ya kara janyo karancin Dalar Amurka a kasar nan.
Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya kara samun koma bayan da ba a taba ganin irinsa ba tun shekarar 2004, inda a farkon makon nan gangar danyen mai ta koma Dala 36.
kasashen da ke amfani da mai na cin ribar wannan faduwar farashi. Sai dai kasashen da ke fitar da mai kamar Najeriya da benezuela da kasashen yankin Tekun Fasha suna fuskantar kalubalen tattalin arziki.