Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zabi Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai masa mataimaki a babban zaben 2023.
Atiku ya bayyana hakan ne a taron da shugabannin jam’iyyar PDP suka gudanar kan zabar wanda zai yi wa jam’iyyar takarar mataimaki a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
- Zan sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba – Yahaya Bello
- Takarar Musulmi 2 a APC: Bai kamata APC ta yi watsi da al’ada ba – Lalong
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya ce jam’iyyar ta kafa kwamitin mutum 17 domin zabar wanda zai yi mata takarar mataimaki.
Ya ce kwamitin ya mika sunayen mutum uku ga Atiku domin ya zaba.
A cewar Ayu, Atiku ne ke da hurumin zabar wanda zai masa mataimaki.
Ifeanyi Okowa, wanda shi ne gwamnan Jihar Delta kuma tsohon Sanatan Delta ta Arewa a Jihar.
Da ya ke jawabi, Atiku ya ce ya zabar mutum daya tsakanin sunayen mutum da aka mika masa, ya kasace abu mai wahala.
Sai dai ya ce ya yi duba da wanda ya fahimci girman kalubalen da kasar nan ke fuskanta da kuma wanda yak e da kwarewa, sannan wanda zai iya samar wa PDP mafita.
Ya ce ya nemi wanda ke da nagarta irin ta shugabanni, wanda zai iya tsayawa a matsayinsa idan ba ya nan.
Atiku y ace Okowa ya fi kowa cancanta daga jerin sunayen wadanda aka gabatar masa.