Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya gargadi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta daina amfani da karfin tsiya ta kowace siga wajen korar masu zanga-zangar kyamar rundunar SARS.
Atiku wanda ya yi takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar PDP, ya bayyana gargadinsa ne cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na Twitter da Facebook.
- Hilary Clinton ta gargadi Buhari a kan kashe masu zanga-zangar #EndSARS
- EndSARS: An fara binciken harbin da ka yi a Lekki
Wazirin Adamawa ya kuma bayyana damuwa a kan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar zangar-zangar da ta rikide ta koma rikici a wasu sassan kasar.
Ya ce, “Kira na ga gwamnatin da Buhari ke jagoranta shi ne kada ta raya mata cewa sai ta yi amfani da karfin tsiya a kan masu zanga-zangar #EndSARS.”
“Masu zanga-zangar EndSARS su na da manufa, don sun yi abin da ya dace kuma wannan shi ne lokaci mafi dace da ya kamata a duba lamarin domin gaggauta biyan bukatunsu.”
“Yin amfani da karfin tsiya babu abin da zai haifar sai harzuka lamarin a madadin ya shawo kansa,”inji Atiku.
Ya kara da cewa, “Idan gwamnati ta nuna damuwarta a kan lamarin, al’umma za su rusuna don yanzu lokaci ne da ya kamata a yi amfani da hankali da basira ba wai karfi da yaji ba.”
Ya kuma nemi Shugaba Buhari da ya fito ya gabatar da jawaban rarrashi ga ’yan kasa musamman matasa.