Dan Takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nada Sanata Dino Melaye a matsayin kakakin yakin neman zabensa.
A wata sanarwa da mai bai wa Atikun shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, ya bayyana sunan Melaye tare da Dokta Daniel Bwala a matsayin wadanda ya bai wa sabbin mukamai.
- Shugaban Ukraine ya nemi tallafin Najeriya a yakinsu da Rasha
- NAJERIYA A YAU: Rawar da matasa za su taka a zaben 2023
“Nade-naden nasu su biyu zai fara aiki nan take,” inji Ibe a cikin sanarwar.
Melaye ya kasance dan majalisar dattawa ta takwas, wanda ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma.
Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke Karamar Hukumar Ijumu a jihar Kogi.
Bwala, a daya bangaren kuwa, kwararre ne a fannin shari’a, dan siyasa kuma manazarci kan harkokin jama’a.
Ya fito ne daga jihar Adamawa.
Bwala, a baya ya kasance jigo a jam’iyyar APC mai mulki, kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP saboda takarar Musulmi biyu da APC ta bai wa Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.