✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya lashe akwatin Gwamnan Gombe

Kuri’a 215 atiku ya samu, yayin da Tinubu na jam'iyyar gwamnan ya tashi da 186

Dan takarar Shugaban Kasa karkashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya doke Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a akwatinsa mai lamaba 010 da ke yankin Jekadafari.

Gwamna Yahaya shi kodinetan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Ahmed Tinubu, a shiyyar Arewa ta Gabas.

Baturen zabe na rumfar, Mishel Thomas shi ne ya ba da sanarwar sakamakon kuri’un da aka kada a akwatin, inda ya ce Atiku Abubakar ya samu kuri’a 215, yayin da Tinubu ya tashi da kuri’a 186.

An ga Gwamna Yahaya tare da matansa, Hajiya Asma’u Yahaya da Hajiya Amina Yahaya a lokacin da suka kada kuri’arsu ranar Asabar da rana.

Shi kuwa dan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, kuri’u 10 ya samu a kwatin, sannan Peter Obi na Jam’iyyar Labour ya samu hudu.