Rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa ta kama matasa huɗu da ake zargin ƴan Boko Haram ne dake shirin kai hari ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Abdurrasheed Shehu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta ce “muna son sanar da ƴan Najeriya cewa da kimanin 9:44 na dare, ranar Lahadi, Yuli 23, 2023 aka kama wani mutum a ƙofar gidan Atiku Abubakar dake Yola.
Atiku Abubakar ya shawarci Musulmi su kwato addinin daga masu tsatstsauran ra’ayi
Ban amince da sakamakon zabe ba –Atiku Abubakar
“Mutum ya shaidawa ƴan sanda cewa sunansa Jubrila Mohammed mai shekaru 29 kuma ɗan Boko Haram ne daga Damboa a jihar Borno.
“Ya kuma shaida musu cewa shi da wasu takwarorinsa uku, waɗanda su ma aka cafke su daga bisani, sun shirya kai hari ne kan wuraren dake da alaƙa da Atiku Abubakar.
“Tuni dai aka miƙa mutane huɗun da ake zargi zuwa ga rundunar soji.
Sanarwar ta kuma yaba wa rundunar ƴan sanda bisa wannan ƙoƙari tare da da kira ga hukumomin tsaro su ci gaba da mayar da hankali kan aikinsu.