✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU za ta maka gwamnati a kotu kan yanke albashi

ASUU na shirin maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan yanke albashin watan Oktoba da aka yi wa lakcarori.

Kungiyar Malam Jami’a (ASUU) na tunanin maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan yanke albashin watan Oktoba da aka yi wa lakcarori.

Bayan taron gaggawa da kungiyar ta kammala a safiyar Talata, Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osedeke, ya soki biyan su albashin kwana 18, yana mai cewa su ba ma’aikatan wucin gadi ba ne ballantana a ce iya ranakun da suka yi aiki kadai za a biya su.

Farfesa Osedeke ya ce, “Kungiyar za ta ci gaba da bin matakan da doka suka dace na shawo kam matsalar ba tare da ta sarayar da muradu da kuma walwalar malaman jami’a ba.”

A cewarsa, abin da gwamnati ta yi musu ya saba duk wata dokar kwadago da tsarin aikin malaman duniya da aka sani a fadin duniya.

Duk da cewa bai ce uffan game da shiga sabon yajin aiki ba, Farfesa Osedeke, ya yi kira ga iyaye da dalibai da sauran ’yan Najeriya da su fahimci matsayin lakcarorin.

A cewarsa, biyan su iya kwanakin da suka yi aiki kamar ma’aikatan wucin gadi, abu ne da ba a taba yi ba a taririn aikin koyarwa a jami’a.

Ya ce, ASUU ta janye aiki ne domin biyayya ga umarnin kotu da kuma la’akari da kokarin ’yan kasa masu kishi, ciki har da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.
Ya ce sun janye yajin aikin bisa yakinin cewa bangaren shari’a zai yi adalci sannan sauran bangarorin gwamnati za su yi abin da ya kamata da kishin kasa domin sasanta da kungiyar cikin ruwan sanyi.

Amma abin da gwamnati ta yi musu na biyan albashi kamar masu aikin wucin gadi na bukatar su dauki matakin doka.