Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige ya bayar da tabbaci cewa Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) za ta janye yajin aikin da take yi a watan Janairun 2021 mai kamawa.
Ngige ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya riga ta biya kusa dukkannin bukatun malaman jami’a, saura dan abin da bai taka kara ya karya ba.
- An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya
- Sojoji ne suka ceto Daliban Kankara —Fadar Shugaban Kasa
- Mutumin da ya kera kofar Dakin Ka’aba ya rasu
“Mun biya kashi 98 cikin 100 na bukatun ASUU; kashi 2 cikin 100 da ya rage kuma shi ne ake alkawari.
“Ina kyautata zaton zuwa karfe 12 na dare ranar Litinin akwai ayyukan da za mu yi; su ma da wanda za su yi a bagarensu”, inji Ministan Ilimin.
Ya ce bangaren gwamnati da ASUU za su tattauna kan ragowar kashi biyun bukatun malaman a zaman da bangarorin za su yi ranar Talata.
Ya ce bayan tattaunawar ana sa ran ASUU ta janye yajin aikinta a ci gaba da karatu a jami’o’i a watan Janairun 2021.
“Ranar Talata za mu tattauna, mu kuma hada abin da muke da shi da wadanda suke da shi na bayanai; na tabbata da zarar mun tattauna maganar yajin aiki ta kare,” inji Ngige.
A watan Maris ne malaman jami’a karkashin kungiyar ASUU suka fara yajin aiki domin neman biyan bukatunsu.
Bukatunsu sun hada da soke batun sanya su a tsarin albashi IPPIS na bai-daya da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi; biyan alawus din da suke bin bashi; da kuma samar wa jami’o’i wadatattu kudade da sauransu.