Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta yi barazanar shiga yajin aiki idan Gwamnatin Tarayya ta gaza duba albashin mambobinta tare da samar da isassun kuɗaɗen Jami’o’i.
A yayin wani taron manema labarai a Uyo da aka yi a ranar Litinin, Kwamared Happiness Uduk, Shugabar ASUU ta shiyyar Kalaba, ta bayyana damuwarta a madadin shugabannin jami’o’i daban-daban.
- Kotu ta hana ’yan sanda da sojoji fitar da Sanusi daga fada
- ’Yan Sanda Sun Kama Sojoji 4 Kan Fashi Da Makami
Uduk, ta ce tun bayan shekara 15 ba a sake duba albashin malaman jami’o’i ba, duk da wasu sassa kamar majalisa, ‘yan sanda da sojoji da kuma ɓangaren shari’a an sake tattaunawa kan albashinsu sau da yawa.
Ta kuma koka da cewa tun farkon fitar da Naira biliyan 200 daga cikin Naira tiriliyan 1.3 da Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin farfaɗo da jami’o’in gwamnati a 2013, ba a sake fitar da wasu kuɗaɗe ba.
Wannan ya sha bamban da yadda gwamnati ke kashe Naira biliyan 90 a aikin hajji tare da yin watsi da fannin ilimi, in ji ta.
A halin da ake ciki, ASUU reshen Abuja ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda ake ci gaba da biyan albashin mambobin kungiyar ta hanyar tsarin biyan albashi na IPPIS.
Ta koka duk da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na cire manyan makarantu daga tsarin na watanni huɗu da suka gabata.
Shugaban Ƙungiyar ASUU na shiyyar Abuja, Salahu Mohammed Lawal ne, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Shiyyar ta ƙunshi Jami’ar Abuja; Jami’ar Tarayya, Lafiya; Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna; Jami’ar Ibrahim Badamasi, Lapai, Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi.