✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

ASUU ta ce biyu daga cikin alkawuran da gwamnati ta dauka kawai ta iya aiwatarwa.

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki saboda gaza cika alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta dauka a yarjejeniyar da suka kulla a bara.

Saka malaman a tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma kin biyansu albashin daga bisani ya yi sanadin shigarsu yajin aikin har kusan wata goma a bara.

Daga bisani dai kungiyar ta janye yajin aikin a watan Disambar 2020 bayan cimma matsaya da gwamnati.

Shugaban ASUU reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Dokta Ibrahim Ibrahim Inuwa ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a makarantar.

Ya ce sun janye yajin aikin a bara ne sakamakon yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati tare kuma da lokacin aiwatar da ita.

“Sai dai abubuwa biyu ne daga cikin wadanda aka amince gwamnatin ta iya aiwatar da su,” inji shi.

Dokta Ibrahim ya yi bayanin cewa sauran alkawuran da gwamnatin ta gaza cikawa sun hada da biyan kudaden alawus-alawus na EAA, saka kudade a Asusun Kula da Jami’o’in Gwamnati, yawan karkafa jami’o’in Jihohi da kuma maye gurbin tsarin biyan albashi na IPPIS da na UTAS.

A cewarsa, kamata ya yi a ce gwamnati ta saki kudaden alawus-alawus din na EAA tun a watan Mayun da ya gabata, amma har yanzu ta ki cewa uffan a kai.

Shugaban na ASUU ya kuma ce a wancan lokacin gwamnatin da kanta ta amince zata maye gurbin IPPIS da UTAS bayan ta amince da shi.

Sai dai ya ce jim kadan da cimma matsayar, wakilan Gwamnatin Tarayyar suka fara yunkurin yi wa tsarin zagon kasa don ganin bai kai ga gaci ba.

Ya kuma zargi Ofishin Babban Akanta na Najeriya da yin amfani da IPPIS wajen cire sunan mambobinsu daga tsarin biyan albashi, yayin da wasu kuma aka zaftare musu nasu.