Kungiyar Malaman jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta ce ba ta amince wani malamin jami’a ya yi aiki a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa ba.
Kungiyar ta ce ta janye daga yin aiki a duk wani zabe da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) za ta shirya saboda matsalolin da ke tattare da zabukan.
Kungiyar ta ce ta bukaci INEC ta ba ta damar sanya ido a dukkan matakan zabe, kama daga rumfunan zabe zuwa wajen kidaya kuri’u da sanarwa amma gwamnatin tarayya ta yi watsi da wannan bukata ta ASUU.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa Emmanuel Osadeke ne, ya bayyana haka a wata tattaunawa da jaridar Punch a ranar Lahadi, inda ya ce tun a lokacin da Farfesa Mahmud Jega ke shugabancin hukumar zabe ne suka yanke shawarar daina yi wa hukumar aiki.
Sai dai ba a sani ba ko wannan matakin na da alaka da yajin aiki da kungiyar ke yi wa Gwamnatin Tarayya kan gaza cika mata alkawuran da ta dauka mata a baya.